Fasinjojin jirgin kasa Abuja-Kaduna sun taka da kafa zuwa Rigasa yayinda jirgin ya lalace da daddare

Fasinjojin jirgin kasa Abuja-Kaduna sun taka da kafa zuwa Rigasa yayinda jirgin ya lalace da daddare

Fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja sun shiga halin ha'ula'i yayinda jirgin ta samu matsala cikin daji kusa da tashan RIgasa wanda ya tilastasu takawa da kafa zuwa tashan karshe.

Wasu fasinjojin sun bayyana manema labarai cewa jirgin ya tashi daga Abuja misalin karfe 6 na yamma amma ta samu matsala kimanin mita 100 da Rigasa misalin karfe 8 na dare.

Daya daga cikin fasinjojin mai suna Sani Lawal, ya bayyana cewa: "Ma'aikatan sun fada mana cewa sai an dauki sa'o'i uku kafin wata jirgi ta zo daga Abuja domin karasawa damu. Sai mutane suka fara fitowa kawai suna takawa zuwa Rigasa."

Duk da cewa hukumar jiragen kasa basuyi tsokaci kan lamarin, wasu jami'an da suka bukaci a sakaye sunayensu sun ce fasinjojin sun isa lafiya saboda babu nisa zuwa tashan.

"Nisan babu yawa, kuma za'a bukaci akalla sa'o'i uku kafin wani jirgin ya iso. Sai suka yanke shawaran daukan kayayyakinsu su taka kawai." Yace

Fasinjojin jirgin kasa Abuja-Kaduna sun taka da kafa zuwa Rigasa yayinda jirgin ya lalace da daddare

Fasinjojin jirgin kasa Abuja-Kaduna sun taka da kafa zuwa Rigasa yayinda jirgin ya lalace da daddare
Source: Facebook

Wannan ba shi bane karo na farko da jirgin ke samun matsala ba musamman da daddare.

Za ku tuna cewa cewa a watan Satumban 2017, jirgin ya turmushe shanaye 50 a dajin Rijana.

Hankulan fasinjojin sun tashi lokacin saboda Rijana ta shahara da yan fashi da masu garkuwa da mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel