Tirkashi: An cafke wata mata dauke da ATM 23 boye a 'gabanta'

Tirkashi: An cafke wata mata dauke da ATM 23 boye a 'gabanta'

Jami’an ‘yan sanda sun cafke wata mata mai shekaru 23 a duniya ‘yar kasar Tanzania, a kan zargin ta da da ake yi da satar kudin mutane daga asusun bankunansu ta hanyar amfani da ATM dinsu.

Wacce ake zargin mai suna Halima, an kamata ne a ranar Talata 16 ga watan Nuwamba, bayan da ta yi amfani da katikan ATM daban-daban wajen cire kudi daga banki.

Halima dai ta yi kokarin tserewa bayan da aka kamata da katikan ATM 23 na mutane daban-daban boye a gabanta.

“A ranar 25 ga watan 2019, wani Ernest Mika Sakala, ya kawo karar wata mata mai wacce bai sani ba ofishin ‘yan sandan da ka Mbagala Maturubai. Ya bayyana yadda matar wacce bai sani ba ta canza masa ATM dinsa da wani. A lokacin da ya je cire kudi, sai ya gano cewa ba katin ATM dinsa bane a tare dashi. Ya kuma gano cewa an cire wasu kudi daga asusun bankinsa,” shugaban ‘yan sandan yankin Dar es Salaam ya sanar.

DUBA WANNAN: Kishi: Yadda matar aure ta antayawa tsohuwar matar mijinta ruwan zafi a fuska

Rahoto daga K24Tv ya nuna cewa, Halima ta amsa cewa tana cikin barayin ATM din mutane, wacce ke wawushe musu kudin asusun bankinsu. Ta kan samu katikan ne ta hanyar rashin gaskiya.

“Ta bayyana yadda ta ke zuwa da zummar taimako ga tsoffi amma wadanda basu yi karatu ba. Sai ta nuna zata taimaka musu, amma sai ta karbe katin tare da musu karyar cewa injin ya hadiye musu kati. Daga baya sai ta je injin cire kudin don kwashe musu kudin da ke asusunsu,”

Wata hanya kuma da suke amfani da ita wajen damfarar mutane itace, zasu tsaya a bayan mai cire kudi daga injin. Idan mutum ya ciro kudin yana kirgawa sai suyi wuf su canza masa ATM dinsa da wani daban,” kamar yadda Mambosasa ya sanar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel