Bidiyon wani da ya fito da mazakutarsa ya yi barazanar yi wa ma'aikaciyar wutan lantarki fyade

Bidiyon wani da ya fito da mazakutarsa ya yi barazanar yi wa ma'aikaciyar wutan lantarki fyade

Wani fusataccen mutum ya cire wandonsa tare da hanzarta fito da mazakutarsa. a yayin da yake wa wata ma'aikaciyar kamfanin wutar lantarki barazanar fyade. Ma'aikaciyar ta yanke masa wutar gidansa ne.

A bidiyon da ya yawaita a kafafen sada zumuntar zamani, an ga mutumin na korafi a fusace a kan yadda aka tsinke masa wayar wutar lantarkin da ke kaiwa gidansa.

An gano ma'aikaciyar kamfanin wutar lantarkin ta PHCN, rike da wayar da ta cire a kafadarta yayin da mutumin ke kokarin kwace wayar. Matar ta yi mirsisi ta hana mutumin wayar wutar lantarkin.

Mutumin ya cigaba da ikirarin cewa, dan sa ya taba rasa ransa bayan an cire masa wayar wutar lantarkin.

DUBA WANNAN: Kishi: Yadda matar aure ta antayawa tsohuwar matar mijinta ruwan zafi a fuska

Wani ma'aikacin kamfanin wutar lantarkin ne ya nadi bidiyon mutumin tare da matar wacce ta ki sakin wayar, shi kuma yana barazanar yi mata fyade.

Mutane da yawa da ke wajen sun yi tsammanin barazana ce kawai, har sai lokacn da ya cire wandonsa tare da bayyana mata mazakutarsa.

Tuni dai masu kallo suka fara gudu daga inda lamarin ke faruwa bayan da suka ga ya cire wandon. Ma'aikaciyar kamfanin wutar lantarkin kuwa, ta saki wayar tare da wucewa ta bashi waje.

Bayan nan ne ta bayyana kujewar da ta yi a kafadarta yayin kokarin kwace wutar lantarkin daga hannun mutumin.

An ji muryoyi daga bidiyon inda wasu ke kiran mutumin da ''mahaukaci" amma bai damu ba. A maimakon hakan kuwa, ya cigaba da korafi a kan ma'aikatan kamfanin wutar lanatarkin yayin da yake mayar da wandonsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel