Mutane sun caccaki Zahra Buhari a kan kudin shiga taron ganawa da ita da ta tsauwala

Mutane sun caccaki Zahra Buhari a kan kudin shiga taron ganawa da ita da ta tsauwala

- Zahra Buhari Indimi,'yar shugaban kasa kuma matar shahararren dan kasuwa Ahmed Indimi, ta shirya taron karawa juna sani

- Za a yi taron ne a ranar 30 ga watan Nuwamba kuma za a tattauna ne a kan tsangwamar ko ba'a a yanar gizo

- Kudin shiga wajen N10,000 ne, lamarin da ya jawo mata caccakadaga mutane da yawa

‘Yar shugaban kasa kuma matar sanannen dan kasuwa, Zahra Buhari Indimi ta shirya wani taron kara wa juna sani game da matsalar tsangwama a Intanet musamman ga mata.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na instagram, Zahra za ta bayyana irin halin da ta samu kanta a hannun masu amfani da kafafen sada zumuntar zamani suna tsangwama ko tsokanarta.

Hakazalika, bakin da ta gayyata zasu bayyana nasu ra’ayin.

Wannan lamarin yajawo cece-kuce ga ‘yar shugaban kasar saboda kudin shiga gurin da ta sa har N10,000.

DUBA WANNAN: Kauye: Gwamnatin Zamfara ta dauki alkawarin kara wa 'yan bautar kasa alawus

Manema labarai sun yi kokarin jin ta bakin matar shahararren dan kasuwar amma abun ya ci tura.

Amma a rubutun da ta wallafa a shafinta na Instagram din, tace kudin zai shiga gidauniyarta ne na ZMB Homes.

Akwai labarina da nake ta son in bayar. Labari ne a kan kwarin guiwar da na samu duk da tsangwama da ba’a da na fuskanta a intanet, kuma nasan kuna dashi,” cewar Zahra.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel