Zaben Kogi: Edward Onoja ya jaddada goyon baya ga Ubangida Yahaya Bello

Zaben Kogi: Edward Onoja ya jaddada goyon baya ga Ubangida Yahaya Bello

‘Dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kogi, a zaben da ya gabata, Mista Edward Onoja, ya fito ya tabbatar da mubaya’arsa ga Mai gidansa gwamna Yahaya Bello a wata doguwar wasika.

A wannan wasika da mu ka samu labarin ta a Jaridar Daily Trust, Edward Onoja, ya kira gwamnan da Ubangida, Aboki, Tagwai, Mai-ceto, tare da gode masa kan yadda aka yi zaben jihar.

Tsohon shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamnatin ya zama mataimakin gwamna a APC tare da Yahaya Bello bayan ya ajiye mukaminsa. An yi hakan ne bayan tsige Elder Simon Achuba.

Onoja ya godewa Mai girma gwamna Bello wanda ya ce zuwansa ya kawo karshen wasu Miyagu da su ka yi kabe-kabe a gidan gwamnatin jihar Kogi kafin Ubangiji ya kudurta zamansa gwamna.

“Shekaru hudu na mulkin Yahaya Bello a Kogi ginin turaku ne aka yi wajen kawo cigaba a jihar.” Onoja ya ce: “Na yi imani Ubangiji zai cigaba da kare mu a wannan hanya da aka kama.”

KU KARANTA: Shugabannin addinai sun soki zaben Kogi, sun ce yaki aka yi

Wasikar ta ce: “Ina gode maka da ka yi watsi da matsin lambar fifita wata Kabila domin murkushe wadanda ba Anebira ba. Ka zama abin koyi da ka zabi ka tafi da kowa domin samun hadin kai.”

“Mu masu bautar Yesu, mun gode maka na bada kwangilar gina coci a cikin gidan gwamnati, wanda wannan ya sa Kogi ta zama cikin daidaikun jihohin da kowane addini ke da wurin ibada.”

“Mu na godiya da gagarumin aikin da ka ke yi na gina abubuwan more rayuwa bayan dogon gibin da ka gada. Mu na godiya game da gyaran da ka ke kawowa a harkar ma’aikatan gwamnati.”

A karshen wannan takarda mai tsawo, mataimakin gwamnan na Kogi, ya nuna cewa har gobe ya na tare da jan zakin mai gidan na sa, tare da yi masa addu’ar mafificin sakayya daga Ubangiji.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel