Buhari, Osinbajo, Boss, Abba Kyari da ministoci sun halarci taron majalisar zartarwa

Buhari, Osinbajo, Boss, Abba Kyari da ministoci sun halarci taron majalisar zartarwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci zaman majalisar zartarwa daya hada kafatanin ministocin gwamnatin Najeriya, daya gudana a ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamba a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa.

Legit.ng ta ruwaito ana gudanar da taron majalisar ministocin a babban dakin taron fadar gwamnatin Najeriya, a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Buhari, Osinbajo, Boss, Abba Kyari da ministoci sun halarci taron majalisar zartarwa

Buhari, Osinbajo, Boss, Abba Kyari da ministoci sun halarci taron majalisar zartarwa
Source: Facebook

KU KARANTA: Alkali ya yanke hukuncin daurin wata 6 ga matashin daya saci wayar salula a Masallaci

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Gida Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Najeriya, Abba Kyari da kuma shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Daga cikin ministocin akwai ministar kudi, Hajiya Zainab Ahmed, karamar ministan tama da karafa Uchechukwu Ogah, ministan wasanni Sunday Dare, ministan sadarwar Isah Pantami, ministan ilimi Adamu Adamu, ministan Neja Delta, Godswil Akpabio da dai sauransu.

Buhari, Osinbajo, Boss, Abba Kyari da ministoci sun halarci taron majalisar zartarwa

Buhari, Osinbajo, Boss, Abba Kyari da ministoci sun halarci taron majalisar zartarwa
Source: Facebook

Idan za’a tuna a daren Laraba, 27 ga watan Nuwamba ne wasu gungun miyagu yan bindiga sun yi awon gaba da Alhaji Mohammed Ibrahim Pada, hakimin garin Rubochi na karamar hukumar Kuje dake babban birnin tarayya Abuja.

Baya ga sace hakimin, yan bindigan sun raunata yaran hakimin guda biyu bayan sun sassaresu da adda a yayin da yaran suka yi kokarin ceto mahaifin nasu daga hannun barayin.

Buhari, Osinbajo, Boss, Abba Kyari da ministoci sun halarci taron majalisar zartarwa

Buhari, Osinbajo, Boss, Abba Kyari da ministoci sun halarci taron majalisar zartarwa
Source: Facebook

A wani labarin kuma, a ranar Talata, 26 ga watan Nuwamba ne gwamnatin jahar Zamfara ta soke dokar da ta tilasta ma gwamnatin jahar Zamfara biyan tsofaffin gwamnoni miliyoyin kudade a matsayin kudin fansho, tare da haramta biyan gaba daya.

Wadanda suke amfana da wannan doka sun hada da tsofaffin gwamnoni, tsofaffin mataimakan gwamnoni, tsofaffin kaakakin majalisa, tsofaffin mataimakan kaakakin majalisa, inda gwamnati ke biyansu makudan miliyoyi a duk wata da kuma sauran alfarma daban daban.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel