Yanzu-yanzu: Rikici ya barke tsakanin yan Shi'a da yan sanda a Abuja, an kashe yar makaranta

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke tsakanin yan Shi'a da yan sanda a Abuja, an kashe yar makaranta

Wata yarinyar yar makarantar sakandare ta rasa rayuwarta a ranar Laraba yayinda rikici ya barke tsakanin yan kungiyar Shi'a da suke gudanar da muzahara a kasuwar Wuse, birnin tarayya Abuja.

Yarinyar, dalibar Government Secondary School, Wuse ta gamu da ajalinta ne yayinda take komawa gida daga makaranta.

Wani mai idon shaida ya bayyana cewa wani jami'in dan sanda mai suna, Geoffrey A. Rafah, ne ya bindige yarinyar bisa kure amma Legit.ng bata tabbatar da ikirarinsa ba.

Hakazalika, yan sanda sun garkame yan jarida biyu dake dauka hotunan abinda ke faruwa. Daga cikinsu akwai Afolabi Sotunde na Reuters.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel