Tirkashi: Karuwa ta cakawa saurayinta wuka ya mutu har lahira bayan yayi mata cikin shege yace a zubar da shi baya so

Tirkashi: Karuwa ta cakawa saurayinta wuka ya mutu har lahira bayan yayi mata cikin shege yace a zubar da shi baya so

- Wani mutum mai suna Seun ya ci karo da ajalinshi ne a hannun karuwarshi

- Rigima ta sarke tsakaninsu saboda ta samu ciki amma ya bukaci a zubar

- Hakan ya fusatata inda ta dau wuka ta soka mishi, washegari ya ce ga garinku

Wani mutum mai suna Seun ya hadu da ajalinshi, bayan da karuwarshi ta soka mishi wuka saboda ta samu juna biyu.

Lamarin ya faru ne a Ilesha, jihar Osun. Rigima ta sarke tsakanin Seun da karuwarshi ne bayan da ta samu juna biyu amma sai ya bukaci a zubar. Ya yi hakan ne saboda yana da mata da yara biyu.

Amma wannan shawarar sai ta fusata budurwar Seun din, wanda hakan ya jawo musu rigimar. A yayin rigimar ne ta samu wuka ta soka mishi, lamarin da ya jawo mutuwarshi washegari. Tuni dai ‘yan sanda suka cafke karuwar.

KU KARANTA: Amfanin ruwa guda 10 a jikin mutum idan ya sha da safe kafin ya fara cin abinci

Wannan dai ba sabon lamari ba ne a Najeriya, musamman ma wajen mazaje masu aure, inda za su bar matansu na Sunnah su fita su tafi neman karuwai a titi.

Sai dai wasu suna ganin cewa hakan yana da nasaba da yanayin matan namu na Najeriya, inda da yawa basu da kwarewa wajen rike miji, hakan yake tilasta mazajen na su fita su fara neman matan banza a titi.

Ita dai wannan karuwa lamarin na ta yayi kamari tunda har ta kai ga kisan kai, yanzu haka dai tana hannun 'yan sanda za su kammala bincike su kuma tura ta kotu domin a yanke mata hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel