Dalilan da yasa arewa zata iya cigaba da mulkin Najeriya har abada - Doyin Okupe

Dalilan da yasa arewa zata iya cigaba da mulkin Najeriya har abada - Doyin Okupe

Doyin Okupe, tsohon kakakin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya nuna cewar mulkin Najeriya kan iya dawwama a yankin arewa.

Okupe ya bayyana cewa rashin hadin kai a tsakanin jihohin kudancin Najeriya, shine abinda zai cigaba da bawa arewa damar cigaba da mulkin kasa har abada.

Ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga kalaman mukaddashin shugaban kungiyar tuntuba ta arewa (ACF), Alhaji Musa Liman Kwande, wanda ya bayyana cewa 'yan zasu zabi dan takarar da ya fito daga yankinsu ne a zaben shekarar 2023.

A wani rubuta da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta (Facebook), tsohon kakkin ya bayyana cewa rashin hadin kai a tsakanin 'yan siyasar yankin kudu zai cigaba da bawa 'yan siyasar arewa dama su cigaba da mulkin Najeriya.

"A 'yan kwanakin baya bayan nan ne shugaban kungiyar ACF ya fito ya bayyana cewa 'yan arewa zasu zabi dan takarar shugaban kasa ne da ya fito daga yankinsu a shekarar 2023 ba tare da la'akari da banbancin jam'iyyar siyasa ba. Kalamansa ya fusata 'yan siyasar kudancin Najeriya, lamarin da yasa suka dora alhakin karfin gwuiwar da ACF ta samu na fadin hakan a kan rashin hadin kansu.

"Maganar gaskiya shine zai yi wuya a samu hadin kai a tsakanin 'yan siyasar kudu. Hakan kuma ya zama riba ga arewa. Ana samun mafi rinjayen kuri'u ne daga yankin arewa maso yamma (NW) saboda sun dauki kansu a matsayin al'umma daya. Duk da akwai banbancin harshe da al'adu, mutanen yankin arewa maso gabas (NE) suna bawa yankin NW goyon baya koda yaushe saboda dalilan addini da yare.

"Shi kuma yankin arewa ta tsakiya (NC) bashi da murya daya saboda kananun banbance da ke tsakanin kabilun yankin.

"Idan ka dawo kudu, akwai banbance-banbance a tsakanin mutanen kudu maso kudu (SS), kudu maso yamma (SW) da kudu maso gabas (SE) - kusan kowanne yanki yana zaman kansa tamkar wata kasa daban.

"Ba za a samu hadin kai a tsakanin al'ummar kudu ba kamar yadda za a samu a tsakanin mutanen arewa. Mutumin da ke Warri a jihar Delta ko mutumin da ya fito daga Izon a jihar Bayelsa ko dan kabilar Igbo daga jihar Umuahia, ba zai taba yarda cewa idan dan kabilar Yoruba yana kan mulki, dan yankinsa ne ke shugabanci ba

"A zahirin gaskiya, rashin adalci ne a yi tsammanin cewa za a iya samun hadin kai a tsakanin 'yan siyasar yankin kudu kamar za a samu a tare da 'yan siyasar arewa," a cewar Okupe.

Okupe ya kara da cewa matukar za a cigaba da tafiya a kan irin tsarin dimokradiyyar da Najeriya ke kai, babu abinda zai hana arewa ta cigaba da mulki har abada. Sai dai, ya bayyana cewa babban kalubalen da arewa zata fuskanta idan ta cigaba da mulki, shine yadda zata tabbatar da hadin kai a tsakanin 'yan kasa.

Source: Legit

Online view pixel