Jirgi ya saba dokar tashi sararin samaniya, ya haura Fadar ‘White House’

Jirgi ya saba dokar tashi sararin samaniya, ya haura Fadar ‘White House’

An shiga cikin wani yanayi a Ranar Talatar nan a babban birnin kasar Amurka, bayan da wani jirgin sama ya keta dokar tashi sararin samaniya, inda ya shiga wuraren da doka ta haramta.

Kamar yadda labarai su ka zo mana daga Jaridun kasar waje, wannan abu da ya auku a Ranar 26 ga Nuwamba, ya sa an yi carko-carko a cikin fadar shugaban kasa, da kuma majalisar Amurkan.

Dole aka yi wuf aka sa jama’a su ka bar harabar majalisar kasar, sannan kuma aka hana shiga da fita a fadar shugaban kasar. An yi wannan ne bayan da aka gaza iya magana da Matukan jirgin.

Ma’aikatan da ke alhakin magana da jirage a yankin ba su iya samun damar saduwa da wannan jirgi ba. Tuni aka yi maza aka tanadi jiragen yaki domin a tuntubi wannan jirgi da ya saba doka.

KU KARANTA: An kashe Sarakuna, an tsere da kananan yara a Arewacin Najeriya

The Independent ta rahoto cewa an ga alamun wasu jami’an tsaron kasar Amurka sun bude dakin da ake ajiye makamai masu linzami. An yi wannan ne duk domin daukin matakin gaggawa.

Wannan abu faru ne da safe har ta kai an bada umarni a dauke kowa daga cikin majalisa da kimanin karfe 8:30 na safe. Bayan rabin sa’a, abubuwa su ka dawo daidai, aka koma bakin aiki.

Jami’an Sojijin saman da ke kula da Arewacin kasar Amurka, NORAD, sun fitar da jawabi, su na cewa Dakarunsu na lura da abubuwan da ke faruwa a ko ina. Yanzu abubuwa sun dawo daidai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel