Dalilan da ke nuna alamun watsewar APC da zarar Buhari ya bar mulki

Dalilan da ke nuna alamun watsewar APC da zarar Buhari ya bar mulki

Yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke wa’adin karshe na kammala mulkinsa, wasu na ganin cewa jam’iyyar APC za ta samu kanta a cikin wani mawuyacin hali zuwa zaben 2023.

Shakka babu, jam’iyyar za ta gamu da cikas sosai bayan ficewar shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda irin farin jininsa. Duk da haka ba a iya yanke cewa jam’iyyar za ta mutu war-was.

Legit.ng Hausa ta kawo wasu dalilan da ke nuna akwai alamun rugujewar APC mai mulki nan gaba:

1. Rashin Magaji

A halin yanzu babu wani wanda zai iya ko ya kama hanyar maye gurbin shugaban kasa Buhari a siyasar Najeriya. Ficewar Buhari za ta ragewa APC farin jini sosai har watakila ta iya fadi zabe. Sai dai kuma cin zabe ba zai yi wa jam’iyyar wahala kamar yadda ya yi mata a lokacin adawa ba.

2. Rashin karfi a wasu Yankuna

Daga cikin matsalolin da APC za ta iya samu shi ne dankare karfinta a yanki guda watau musamman Arewacin Najeriya. Har yanzu jam’iyyar ba ta samu gagarumar karbuwa musamman a Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas ba, ko da dai kwanan nan ta lashe zabe a jihar Bayelsa.

KU KARANTA: 'Yan Majalisar adawa da su ka ji babu dadi a hannun Kotun zabe a 2019

3. Rashin mai fada-a-ji

Wata matsalar da jam’iyyar APC ta iya fama da it ace rashin mai fada-a-ji. A jam’iyyar PDP akwai tsofaffin shugabannin kasa na farar hula da na Soji, da wasu manyan da ake ji da su, da za su iya fitowa su sa-baki idan abubuwa su ka yi kamari. Babu irin wannan masu raba-gardama a APC.

4. Taron gayya

Daga cikin abin da ya jawo faduwar PDP a babban zaben Najeriya a 2015 akwai hadin-gamayyar da aka yi wa jam’iyyar bayan da wasu ‘ya ‘yan ta su ka sauya-sheka. APC na iya gamuwa da irin wannan matsala da ta ci moriyarta a shekarun baya, idan har aka yi mata irin wannan gayya.

5. Rikicin cikin-gida

APC ta yi fama da sabani a cikin-gida a zaben 2019, wanda wannan ya jawo mata matsala a Jihohi irin su Zamfara, Ribas, Imo, Oyo, Ogun da sauransu. Irin wannan rigima ya na iya jawo wasu ‘yan cikin-gida su bangare ko kuma su shiryawa jam’iyyar zagon-kasa a zabe mai zuwa.

6. Boren ‘Yan kasa

Jama’a da-dama su na kokawa da halin tattalin arziki da tsadar rayuwar da ake ciki. Muddin APC ta gaza shawo kan wadannan, mutane na iya kin zaben ta a 2023. Kuma ganin yadda tsofaffin ‘Yan PDP su ke komawa APC, ya na iya sa shakku kan yaki da rashawar da ake ikirari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel