Rundunar soji ta kashe mayakan Boko Haram da ISWAP 9 a hanyar shiga dajin Sambisa

Rundunar soji ta kashe mayakan Boko Haram da ISWAP 9 a hanyar shiga dajin Sambisa

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na atisayen LAFIYA DOLE sun kashe wasu mayakan kungiyar 'yan ta'dda na kungiyar Boko Haram da takwararta ISWAP a jihar Borno.

Jami'in kula da watsa labarai na rundunar soji, Kanal Aminu Iliyasu, shine wanda ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da rundunar soji ta fitar ranar Laraba a hedkiwatarta da ke Abuja.

Iliyasu ya bayyana cewa dakarun soji sun ci karo da mayakan kungiyar ta'addancin ne ranar Talata a garin Sabon Gari, mahadar da mayakan kan taru kafin su shiga dajin Sambisa.

Ya bayyana cewa sojojin sun kashe uku daga cikin direbobin motocin mayakan yayin da wasu suka gudu zuwa cikin jeji.

A cewarsa, an samu alburusan bindiga, kayan abinci da kekuna bayan mayakan sun gudu sakamakon matsin lamabar da suke fuskanta yayin musayar wuta da dakarun soji.

DUBA WANNAN: Rufe iyakokin Najeriya: Obasanjo ya fadi abinda ya faru a mulkinsa, ya gargadi kasar Benin

Iliyasu ya kara da cewa dakarun atisayen OPERATION LAFIYA DOLE na runduna ta 29 da ke aiki a Borgozo da ke karamar hukumar Kaga, sun kashe wasu mayakan kungiyar Boko Haram uku yayin da wasu da dama suka gudu da raunuka a wata arangama da suka yi.

Sannan ya kara da cewa dakarun runduna ta 21 ma sun kashe wani dan kungiyar Boko Haram daya tare da kama bindiga biyu samfurin AK47 a wurinsa a Kwanar Banki da ke yankin karamar hukumar Bama.

"Rundunar soji ta samu kiran ko ta kwana a kan cewa wasu mayakan kungiyar Boko Haram suna hanyarsu ta kai hari kauyen Grijan da ke hanyar Damboa - Chibok.

"Rundunar soji ta hanzarta tura jami'anta, kuma sun iske mayakan kafin su shiga garin, inda yayin musayar wuta aka kashe 'yan ta'addar biyu tare da samun bindinga samfurin AK47 guda hudu da alburusai masu yawa," a cewar Iliyasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel