An samu yamutsi a ofishin INEC yayin da jami'an tsaro suka hana Dino Melaye shiga

An samu yamutsi a ofishin INEC yayin da jami'an tsaro suka hana Dino Melaye shiga

- A yau Laraba ne aka samu hargitsi hadi da tashin-tashina bayan da jami'an tsaro suka hana Sanata Dino Melaye shiga hedkwatar INEC

- An kwace na'urar daukar hoton wani dan jarida amma daga baya an mayar masa bayan da Dino Melaye yasa baki

- Daga baya Sanatan ya samu shiga inda ya ja magoya bayansa da manema labarai cikin hedkwatar INEC din

An samu hargitsi a yau Laraba a hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, yayin da jami'an tsaro suka hana Sanata Dino Melaye da manema labarai shiga don mika karin kokensu.

An kwace na'urar daukar hoton wani dan jarida amma daga baya an mayar masa bayan da Dino Melaye yasa baki.

DUBA WANNAN: Kotu ta tsare kakakin jam'iyyar APC a Zamfara a kan zargin yi wa Matawalle kage da tayar da zaune tsaye

Bayan wasu mintoci, Sanatan ya samu ya shigar da kansa, magoya bayansa da kuma manema labarai cikin ofishin hukumar zaben mai zaman kanta.

A cikin ofishin, Melaye ya tabbatar da cewa ba zai fita ba har sai kwamishinan zabe na kasa ya iso don karbar korafinsa.

Melaye na daga cikin 'yan takarar da suka fito neman kujerar sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma a zaben ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba 2019. Yayi ikirarin cewa zaben ya cika fal da tashin hankula tare da magudin zabe kala-kala.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel