Alkali ya yanke hukuncin daurin wata 6 ga matashin daya saci wayar salula a Masallaci

Alkali ya yanke hukuncin daurin wata 6 ga matashin daya saci wayar salula a Masallaci

Wata kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a unguwar Tudun Wada Zaria ta yanke ma wani matashi, Mohammed Abdullahi hukuncin zaman gidan kaso tsawon watanni 6 a kan satar wayar salula ta N10,000 a Masallaci.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito dansanda mai shigar da kara, Sajan Adamu Yahaya ya bayyana ma kotu cewa barawon ya kutsa kai cikin wani Masallaci dake filin Mallawa, Tudun Wada Zaria da sunan zai yi sallah, amma sai ya sace wayar wani mutumi da kudinta ya kai N10,000.

KU KARANTA: Kiran ruwa: Cin mutuncin gwamna a Facebook ya jefa wani matashi a gidan yari

Dansandan ya cigaba da cewa sauran masallata ne suka ankara, inda suka bi barawon a guje, inda bayan sun kama shi sai suka mika shi ga ofishin rundunar Yansandan Najeriya dake unguwar Tudun Wada Zaria.

“A yayin da muka gudanar da bincike a kanshi, wanda ake zargi da satar wayar ya amsa laifinsa na satar wayar salula daga cikin Masallacin.” Kamar yadda Dansanda Adamu Yahaya ya bayyana ma kotu.

Daga karshe Adamu ya bayyana ma kotun cewa laifin da ake tuhumar barawon ya saba ma sashi na 174 da 139 na kundin dokokin shari’an Musulunci ta jahar Kaduna. Shi ma wanda ake tuhumar, ya amsa laifinsa da bakinsa.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin, Alkalin kotun Malam Iliyasu Muhammad-Umar ya yanke ma Mohammed Abdullahi hukuncin daurin watanni 6 a Kurkuku, tare da zabin biyan taran N7,000.

A wani labarin kuma, wani ma’aikacin banki a Najeriya mai suna Michael Itok ya kira ma kansa ruwa sakamakon wani rubutun batanci da ya yi a kan gwamnan jahar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, inda a yanzu haka yana gidan yari a daure.

A ranar Talata, 26 ga watan Nuwamba ne hukumar tsaron farin kaya, DSS, ta gurfanar da matashi Itok a gaban kotun majistri, inda ake tuhumarsa da rubuce rubucen batanci a kan gwamnan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel