Majalisar Najeriya za ta yi binciken musamman a game da zaben Kogi da Bayelsa

Majalisar Najeriya za ta yi binciken musamman a game da zaben Kogi da Bayelsa

Majalisar tarayya ta dauki matakin binciken rikici da kashe-kashen da ya barke a zabukan da aka yi kwanan nan a jihar Bayelsa da Kogi. Duka majalisun tarayyar sun amince da wannan.

Jaridar Daily Trust ta ce majalisar wakilai ta amince da rokon Honarabul Toby Okechukwu na duba abin da ya auku a zabukan gwamnonin Bayelsa da Kogi, inda aka rasa rayukan Bayin Allah.

Wasu ‘yan majalisar APC irinsu Honarabul Ibrahim Idris Wase, sun nuna ja a game da batun binciken. ‘Yan majalisan na APC masu rinjaye su na ganin ana neman daurawa wasu laifi ne.

Kamar yadda Jaridar ta rahoto, an yi tsit da minti guda a majalisar domin makokin wadanda su ka rasa rayukansu a zaben. Chukwuma Umeoji mai wakiltar Anambra ya kawo wannan shawara.

KU KARANTA: Abin da ya sa Jonathan ya sallamawa APC Jihar sa - Sule

Kakakin majalisar wakilan, Femi Gbajabiamila ya goyi bayan a gudanar da wannan bincike. Sai dai shugaban majalisar kasar yace ka da a kira sunan wata jam’iyya a rahoton da za a fito da shi.

Gbajabiamila ya yi wa kwamitin da za su yi wannan aiki kashedi cewa ka da su sake su kama sunan wata jam’iyya ko ta PDP, APC ko SDP a rahotonsu. Kusan wannan ne matsayar Sanatoci.

Ba a bar Sanatocin kasar a baya ba, domin kuwa irin su George Thompson Sekibo, Enyinnaya Abaribe da Abdullahi Yahaya duk sun koka game da yadda wasu ke jawo rikicin zabe a kasar.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmed Ibrahim Lawan, wanda ya jagoranci zaman, ya yi kira ga jami’an tsaro da su cafke duk wanda aka samu da laifi, su yi kokarin ganin an hukuntasu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Online view pixel