Ku fara shirin kirkirar kotu na musamman – Buhari ga Alkalan kotun koli

Ku fara shirin kirkirar kotu na musamman – Buhari ga Alkalan kotun koli

A Ranar Litinin, 25 ga Watan Nuwamban 2019, Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya fadawa Alkalai su fara kafa turaku na kirkiro kotu na musamman da ake shirin yi a fadin kasar.

Shugaban kasar ya yi wannan kira ne wajen wani taron manyan Alkalan kotun koli da ake yi na bana. Wadannan kotu na musamman da za a kafa, za su taimaka wajen yin shari'a cikin sauri.

Ina ba wannan taro shawara a cikin batutuwanta, ta yi la’akari da tsarin yadda za a kafa kotun da za su saurari kara na musamman, ko kuma ayi amfani da tsofaffin kotu domin wannan aiki.”

Shugaban kasar ya kara da fadawa manyan Alkalan kasar cewa: “A kuma duba yadda za a samar da Alkalai masu gaskiya, domin a rage bata-lokacin da ake samu a wajen gudanar da shari’a.”

Kamar yadda Mai magana da yawun bakin shugaban kasar, Femi Adesina, ya fitar da jawabi, Buhari ya fadawa Alkalai ya na sane da matsaloli da kalubalen da ake samu ta fuskar shari’a.

KU KARANTA: Kotu ta tsare Jigon APC saboda wasu kalamai da ya yi a Zamfara

Shugaban kasa ya ke cewa Alkalan kotun kolin da su ka shirya wannan gagarumin taro cewa ya zauna da Alkalin Alkalai, Ibrahim Tanko-Muhammad, domin ganin shawo kan matsalolinsu.

Adesina ya ke cewa shugaban kasar ya dada da: “Gwamnatin nan ta na da shirin yi wa tsarin dokoki garambawul, ta haka mu ke yi wa dokokin baya kwaskwarima tare da kawo sabbabi.

“Bayan haka, mun zauna da Alkalin Alkalai domin ganin an inganta sha’anin kasafin kudin saboda a biya bukatan masu shari’a.” Shugaban kasar ya nemi Alkalai su kara ba shi hadin-kai.

“Ina kuma goyon bayan kara yawan Alkalan da ke manyan kotu, kotun daukaka kara da kotun koli, domin rage nauyin da ke kan masu shari’a. Kuma zan cigaba da yin haka.” Inji Buhari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel