Masu abu da abun su: Zahra Buhari za ta hada wani gagarumin taro da zai jawo hankula a wannan makon

Masu abu da abun su: Zahra Buhari za ta hada wani gagarumin taro da zai jawo hankula a wannan makon

- Muzanta mutane a yanar gizo ballantana kafafen sada zumunta na zamani, sun yawaita a yanzu ko kuma ya zama ruwan dare

- Zahra Buhari Indimi, ‘yar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta shirya tattaunawa a kan wannan lamarin da ya zama ruwan dare

- Fuskar kungiyar tallafawa masu cutar sikilan, zata tattauna a kan yadda mutum zai kara ma kanshi kwarin guiwa

An haifa Zahra Buhari Indimi a ranar 18 ga watan Disamba, 1994. ‘Ya ce ga shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya hau mulkin kasar nan a ranar 29 ga watan Mayu, 2015. Mata ce wajen sanannen dan kasuwa, Ahmed Indimi. Zahra Buhari ce ‘ya ta biyar a wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Amma kuma wata majiyar ta ce Zahra ’ya ta bakwai ce a wajen shugaban kasar. Matar shugaban kasan ta biyu, Aisha Buhari ce ta haifeta.

Zahra na da kungiyar taimakon kai da kai da ake kira da ACE. Kungiyar na tallafawa masu fama da ciwon sikila ne, yayin da shi kuma mijinta ke cigaba da kasuwancinshi.

Ta zama fuskar kungiyar tallafin ne a Najeriya mai suna ACE wacce ta maida hankali wajen ilimantarwa tare da horarwa, habaka tattalin arziki tare da samar da ingantacciyar kiwon lafiya.

KU KARANTA: Allah Sarki: Bayan sun shafe shekara 7 suna tare ya gano cewa akwai wanda take so tun farko haka yasa ya saketa domin taje ta aure shi

Zahra ta rasa ‘yar uwarta sanadiyyar ciwon sikila. Ta kuma zama sabuwar fuskar kungiyar tallafawa masu cutar sikila wacce Nkechi Azinge ta kirkiro. Azinge matashiyar mai taimakon al’umma ce wacce sarauniya ta karrama.

‘Yar shugaban kasar, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Instagram kwanan nan, ta sanar da cewa zata hada wani bikin tattaunawa mai suna #tattaunawa tare da Zahrah# mai kuma taken “Maraice tare da Zahra” wanda za a yi a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2019.

Zata bada labarin ta a kan muzantawa a yanar gizo tare da yadda mutum zai karfafa wa kanshi guiwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel