Tashin hankali: Dalibin jami'a a Najeriya ya dankarawa malamar shi cikin shege

Tashin hankali: Dalibin jami'a a Najeriya ya dankarawa malamar shi cikin shege

- Kevin dalibi ne a bangaren karatun na’ura mai kwakwalwa, wanda ya fada cikin mummunan tashin hankali da alhini

- Hukumar ladabtarwar jami’a ta kori Kevin sakamakon dirkawa wata malamarshi ciki da yayi, bayan da suka dade suna lalata

- Duk da ya bayyana cewa ba laifinshi bane, ya kasa jure ganin kyakyawar surarta ne wacce ta ke ta jawo ra’ayinshi

Labaran da suke zuwa ma Campus Cam Ug, ya bayyana yadda wani dalibin bangaren karatun na’ura mai kwakwalwa a jami’ar tarayya ta Lafia (Fulafia) ya shiga tsaka mai wuya. Hukumar makarantar ta kori dalibin ne bayan da ta kamashi da laifin dirkawa malamarshi cikin shege.

Hukumar ladabtarwa ta jami’ar ta samu wannan mummunan labarin ne da ya firgita mutane da yawa, kafin ta yanke wannan mummunan hukunci a kan dalibin.

Aika-aikar Kevin ta zubarwa da jami’ar mutunci da kuma nagartar malaman jami’ar baki daya. Mutane da yawa sun fito suna kalubalantar hukuncin da jami’ar ta zartar.

Dalibin da ya gurfana a gaban kwamitin ladabtarwar jami’ar don karabar takardar sallamarsa, ya bayyana cewa wannan kuskuren ba nashi bane shi kadai. Kevin ya yi bayanin yadda malamar tashi ta fara nuna mishi alamun soyayya. Daga baya kuma ta rokeshi da su fara lalata, idan da dama ya yi mata ciki.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda guda 2 sun kuma yi garkuwa da mutane 6 a jihar Adamawa

Ya bayyana yadda malamar tashi ta ke bayyana mishi bukatarta, ta hanyar bin hanyoyin tada mishi sha’awa da kyakkyawar surarta tare da dirinta. Ya ce ba zai iya juya baya ga wannan tayin ba, saboda zai iya fuskantar matsaloli ta wajen malamar tashi. A don haka ne ya bada kai bori ya hau.

Yadda labarin ya zagaye jami’ar ne babu wanda ya sani. Abinda dalibin zai iya tunawa shine yadda aka mishi kiran gaggawa da sassafe, a kan bukatar ya bayyana gaban kwamitin ladabtarwan a lokacin.

A tsorace tare da bukatar sanin abinda ke fauwa ya bayyana a gabansu. A lokacin ya gane mu’amalarshi da malamarshi ba wai ciki kadai ta jawo ba, har da korarshi daga makaranta.

Kevin ya bayyana cewa ya dinga lalata da ita har a cikin ofishinta. A take dalibin ya fadi a gaban kwamitin don rokar alfarma, amma sun fada mishi sun yanke hukuncin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel