Kotu ta tsare kakakin jam'iyyar APC a Zamfara a kan zargin yi wa Matawalle kage da tayar da zaune tsaye

Kotu ta tsare kakakin jam'iyyar APC a Zamfara a kan zargin yi wa Matawalle kage da tayar da zaune tsaye

Sakataren yada labarai na APC a jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Danmaliki Gidan Goga, ya gurfana a ranar Talata a gaban babbar kotun shari'ar musulunci da ke Gusau, a kan zargin sa da ake yi da bata wa Gwamna Matawalle suna tare da neman tayar da kayar baya a jihar.

A yayin gabatar da shari'ar, lauyan Gwamna Matawalle, Barista Ibrahim Haruna ya ce, Danmaliki ya hada taron manema labarai a ranar Asabar da ta gabata, inda ya kalubalanci Gwamna Matawalle tare da neman tada kayar baya a jihar, wanda ya ci karo da sashi na 287 da 142 na dokokin shari'a.

Barista Ibrahim ya sanar da kotun yadda hirar da kakakin jam'iyyar APC ya yi da manema labaran aka wallafata tare da watsa ta a kafafen sada zumuntar zamani. Ya kara da bayanin yadda aka batawa gwamnan suna a sakamakon wannan taron manema labaran. Hakan kuma zai iya kawo tashin-tashina cikin jama'a.

DUBA WANNAN: DSS ta kama hatsabibin mai garkuwa da mutane da ya sace alƙalin kotun daukaka kara

Danmaliki wanda ya taba rike kwamishina a jihar, ya musanta zargin da ake masa bayan da lauyansa, Barista Bello Umar ya bukaci kwafin laifukan. Ya kara da rokar kotun da ta yi watsi da karar ko kuma ta saki wanda yake karewa ta hanyar bada belinsa.

Amma kuma, lauyan Matwalle ya soki wannan bukatar inda ya ce babu tilasci a bada belin wanda ke kare kansa a kundin tsarin mulki, sai dai kuwa idan hujjar da wanda ke kare kansan ta karbu ga kotun, kamar yadda sashi na 300, sakin layi na daya na kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanadar.

Alkali Hadi Sani, ya bayar umarnin a tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali har zuwa ranar 12 ga watan Disamba da za a cigaba da shari'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel