Gwamnatin Zamfara ta soke biyan tsofaffin gwamnoni miliyoyin kudaden fansho

Gwamnatin Zamfara ta soke biyan tsofaffin gwamnoni miliyoyin kudaden fansho

A ranar Talata, 26 ga watan Nuwamba ne gwamnatin jahar Zamfara ta soke dokar da ta tilasta ma gwamnatin jahar Zamfara biyan tsofaffin gwamnoni miliyoyin kudade a matsayin kudin fansho, tare da haramta biyan gaba daya.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kashe jami’in dansanda, sun yi awon gaba da injiniyoyin kasar waje guda 3

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wadanda suke amfana da wannan doka sun hada da tsofaffin gwamnoni, tsofaffin mataimakan gwamnoni, tsofaffin kaakakin majalisa, tsofaffin mataimakan kaakakin majalisa, inda gwamnati ke biyansu makudan miliyoyi a duk wata da kuma sauran alfarma daban daban.

Majalisa ta soke wannan doka ne bayan bayyanar wata wasika da tsohon gwamnan jahar Abdulaziz Yari ya aika ma gwamnatin jahar Zamfara yana neman ta biyashi hakkinsa na fansho, wanda ya kai naira miliyan 10 a duk wata, kamar yadda yace dokace ta tanadi haka, kuma a ranar 23 ga watan Maris na 2019 aka yi dokar.

Da yake gabatar da kudurin soke dokar, jagoran majalisa, Faruk Musa Dosara daga mazabar PDP Maradun 1 ya bukaci sauran yan majalisa su duba kudurin a matakin gaggawa domin kawar da dokar dake bukatar biyan tsofaffin shuwagabannin siyasa makudan kudade, yayin da tsofaffin ma’aikata ke cikin bakar wahala ba tare da samun hakkokinsu ba.

A cewar dan majalisan, tsofaffin shuwagabannin siyasan suna lakume kimanin naira miliyan 700 a duk shekara, wanda a yanzu karfin lalitar gwamnatin jahar ba zai iya biya ba, nan take dan majalisa Tukur Jekada Birnin Kudu ya bayyana cewa akwai bukatar soke dokar domin ba shi da amfani ga jama’an jahar.

Bayan tafka doguwar muhawara zazzafa, kaakakin majalisar, Nasiru Mu’azu Magarya ya bukaci akawun majalisa ya tsallakar da kudurin daga mataki na daya zuwa na biyu, inda nan da nan aka mika kudurin zuwa ga kwamitin majalisa da ya yi kudurin karatu na uku.

Jim kadan aka dawo da shi gaban majalisa, kuma ta amince da shi, kai tsaye aka mika ma gwamnan jahar domin ya rattafa hannu a kanta. Bugu da kari a zaman majalisar na yau ne kaakakin majalisar ya rantsar da sabon akawun majalisa, Shehu Saidu.

Da wannan sabuwar doka, babu wani tsohon shugaban siyasa a Zamfara da zai sake samun sisi daga asusun gwamnatin jahar, sai dai wanda dokar hukumar rarraba arzikin kasa ta ware, inji kaakakin majalisar, Mustapha Jafaru Kaura.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel