'Yan bindiga sun kashe 'dagatai' 2 da shugaban 'Yansakai a jihar Taraba

'Yan bindiga sun kashe 'dagatai' 2 da shugaban 'Yansakai a jihar Taraba

- 'Yan bindiga a jihar Taraba sun kashe dagatan wasu garuruwa biyu da ke karkashin karamar hukumar Karim Lamido

- Bayan kisan dagatan biyu, 'yan bindigar sun kashe shugaban 'Yansakai da karin wasu mutane biyu

- Kazalika, 'yan ta'addar sun yi awon gaba da kananan yara biyar zuwa jihar Filato, mai makwabtaka da yankin

Wasu 'yan bindiga da suka kai hari a karamar hukumar Karin Lamido da ke jihar Taraba sun kashe wasu dagatai guda biyu, shugaban kungiyar 'Yansakai (bijilanti) da sauran wasu mutane biyu.

'Yan bindigar, su kusan 30, dauke da manyan bindigu samfurin AK47 sun kai harin ne da tsakar daren ranar Litinin, kuma sun kashe dagacin garin Bilango 1 da na Bilango 2 da ke yankin tsohuwar masarautar Muri.

Daily Trust ta rawaito cewa yan bindigar sun kai harin ne domin daukar fansar kisan wasu masu garkuwa da mutane da 'yan farauta da 'Yansakai suka yi a yankin.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa 'yan bindigar sun kashe masu sarautar gargajiyar da sakatarorinsu a fadarsu, sannan kuma sun kashe shugaban kungiyar 'Yansakai.

DUBA WANNAN: Zaben Bayelsa: Jonathan ya mayar wa da Sule Lamido martani

Dagatan guda biyu da aka kashe sune; Garba Dangari; dagacin garin Bilango 1, da kuma Sarki ali; dagacin garin Bilango 2.

Kazalika, 'yan bindigar sun yi awon gaba da yara biyar daga yankin zuwa jihar Filato, mai makwabtaka da jihar Taraba.

An tura karin jami'an tsaro daga karamar hukumar Karin Lamido zuwa yankin da aka kai harin.

An binne dagatan da sauran mutanen da 'yan bindigar suka kashe da misalin karfe 12:00 na ranar Talata.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa ya zuwa yanzu rundunar 'yan sanda bata kama kowa dangane da kai harin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel