Da duminsa: Kotu ta baiwa yaron Abdulrashid Maina belin N60m

Da duminsa: Kotu ta baiwa yaron Abdulrashid Maina belin N60m

Kwana daya bayan na mahaifinsa, babbar kotun tarayya dake zaune a Abuja ta baiwa Faisal, yaron tsohon shugaban kwamitin gyaran harkan fansho, AbdulRashid Maina, beli

Alkali mai shari'a, Jastis Okon Abang, a shari'ar da ya yanke ranar Talata ya baiwa Faisal beli kan farashin milyan sittin da kuma mai tsaya masa.

Jastis Abanga ya bayyana cewa wajibi ne wanda zai tsaya masa ya kasance dan majalisan wakilan tarayya kuma ya kasance ya mallaki dukiya a Abuja.

Ya ce wajibi ne wanda zai tsaya masa ya rako Faisal kotu duk ranar da kotu ke bukatanshi har zuwa karshen karar.

Ya kara da cewa duk lokacin da wanda ya tsaya masa yaki zuwa kotu, za'a janye belin.

A jiya, babban kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta baiwa Mista AbdulRashid Maina, belin naira bilyan daya tare da mutane biyu da zasu tsaya masa.

Alkalin kotun, Jastis Abang, ta bayyana cewa wajibi ne mutanen zasu tsaya masa su kasance Sanatoci.

Hakazalika, ya ce wajibi da sanatocin biyu su kasance masu gidaje a unguwar Maitama ko Asokoro a cikin birnin tarayya Abuja.

Unguwannin Maitama da Asokoro ne suka fi yawan masu kudi da tsadan gidaje a Abuja.

Bugu da kari, Alkalin ya bayyana cewa wajibi da masu tsaya masa su mika takardan shaidan biyan kudin haraji na tsawon shekaru uku da suka gabata kuma su hallara a kotu a duk ranar da kotu ta bukaceshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel