Yanzu-yanzu: Yadda 'yan sanda suka sumar da wani bawan Allah da duka

Yanzu-yanzu: Yadda 'yan sanda suka sumar da wani bawan Allah da duka

Jami'an 'yan sanda da ke aiki a yankin Anara da ke karamar hukumar Isiala Mbano a jihar Imo sun yi wa wani mutum dukan tsiya har sai da ya yanke jiki ya suma a cewar rahoton da The Punch ta wallafa.

Rahoton ya ce 'yan sandan sun tafi su kama mutumin da ba a bayyana sunansa ba a yammacin ranar Litinin a mahadar St Innocent a Anara kwatsam sai suka fara dukansa a yayin da ya yi yunkurin tambayar dalilin da yasa za a kama shi.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa yayin da 'yan sandan ke dukan mutumin, sauran matasa sun tsere saboda tsoron abinda ka iya kaiwa ya dawo.

A ranar Talata, al'ummar garin sunyi tattaki zuwa ofishin 'yan sanda na Anara inda suka yi zanga-zangar kin amincewa da abinda ya faru da mutumin.

DUBA WANNAN: Bidiyon yadda ake yi wa wata mata na zamani bilicin ya tayar da hankulan 'yan Najeriya

Sun nemi a binciki 'yan sandan da suka yi wa mutumin dukan tsiya da har sai da ta kai ya suma.

Rike da kwalaye, masu zanga-zangan sun koka kan irin cin zali tare da karbar kudade hannun alumma a tilas da 'yan sanda ke yi a garin.

Wani shugaban matasa a garin, Marcel Onuoha, ya ce an garzaya da mutumin zuwa asibiti a Owerri sakamakon kin karbarsa da asibitin farkon ta ki yi.

Ya yi kira da Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu da kwamishinan 'yan sandan jihar, Rabiu Ladodo su binciko 'yan sandan da suk yi wa wannan mutumin duka.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Orlando Ikeokwu ya ce shugabanin hukumar za su dauki mataki a kan lamarin.

Ya yi alkawarin za ayi adalci tare da kira ga mazauna garin su guji daukar doka a hannunsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel