Yan bindiga sun kashe jami’in dansanda, sun yi awon gaba da injiniyoyin kasar waje guda 3

Yan bindiga sun kashe jami’in dansanda, sun yi awon gaba da injiniyoyin kasar waje guda 3

Wasu gungun miyagu yan bindiga sun yi awon gaba da injiniyoyi guda 3 yan kasar China dake aiki a wani sansanin hakar ma’adanan kasa dake yankin Itagunmodi na jahar Osun, bayan sun kashe wani jami’in rundunar Yansandan Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 25 ga watan Nuwamba, inda mazauna garin suka bayyana kaduwarsu game da aukuwar lamarin sakamakon basu taba ganin irin wannan tashin hankali ba.

KU KARANTA: Jiya ba yau ba: Gwamna Masari ya bada labarin yadda Buhari ya shiga aikin Soja

Wani babban jami’in tsaro a jahar Osun daya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa baya ga yan kasar China guda uku da yan bindigan suka sace, sun bindige wani daban a yayin da yayi kokarin tserewa.

“Chanisawan suna wajen hakar ma’adanan kasar suka gudanar a wani aiki ne a lokacin da yan bindigan suka bayyana, inda suka bindige daya, sa’annan suka yi awon gaba da guda uku, a yanzu haka wanda aka harba yana samun kulawa a asibitin koyarwa na jami’ar OAU ile-Ife.” Inji shi.

Majiyarmu ta yi kokarin jin ta bakin kwamishinan Yansandan jahar Osun, Uwargida Abiodun Ige game da lamarin, sai dai hakanta bai cimma ruwa ba, amma wasu majiyoyi daga rundunar Yansandan jahar sun tabbatar da lamarin, kuma sun bayyana an tura kwararrun jami’ai dake bin sawun yan bindigan.

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagun yan bindiga sun dira babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja na jahar Kogi, inda suka tare wata motar bus, suka kashe direban motar, sa’annan suka yi awon gaba da fasinjoji 13 zuwa cikin daji.

lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:12 na yammacin Litinin, 25 ga watan Nuwamba a daidai kauyen Sabon-Gari inda yan bindigan suka fito daga cikin wani daji sanye da kayan Sojoji, kamar yadda wani direba mai suna Ibrahim ya bayyana.

Ibrahim yace yana kan hanyarsa ta zuwa kasuwar Kwairta ne bayan ya fito daga garin Abaji, kwatsam sai ya ci karo da yan bindigan sun fito daga daji sanye da kayan Sojoji, nan take suka shiga bude ma motoci wuta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel