Rotimi Akeredolu ya yi tir da sashen kisa a kudirin yaki da kalaman kiyayya

Rotimi Akeredolu ya yi tir da sashen kisa a kudirin yaki da kalaman kiyayya

Hukumar dillacin labarai na kasa ta rahoto Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo ya na sukar hukuncin kisan da aka yanke a cikin kudirin da zai takawa masu kalaman kiyayya burki.

Rotimi Akeredolu ya bayyana wannan ne a jawabinsa wajen wani taro da cibiyar zaman lafiya da nazari na musamman na CPSS da ke Jami’ar tarayya ta Garin Ilorin, watau UNILORIN ta shirya.

Mai girma gwamnan ya yi magana ne a kan manufofin nan 16 na tsarin SDG na majalisar dinkin Duniya. Daga cikin manufofin shirin SDG akwai adalci da zaman lafiya da karfafa hukumomi.

Gwamnan na APC ya ce bai dace a yankewa mai magana a dandalin sada zumunta hukuncin kisa ba, gwamnan ya ce ko wani irin abu ake yadawa a kafafen, za su zo su bace bayan lokaci.

A ra’yin gwamnan na jihar Ondo, kotu kadai ke da ra’ayin hukunta ‘yan jarida idan har sun saba doka. Akeredolu ya ce wannan ba aikin zababbun shugabanni da ‘yan majalisan Najeriya bane.

KU KARANTA: Shugaban APC ya nemi Gwamnoni su ba Gwamnatin Buhari goyon baya

A jawabin na sa, Gwamnan ya yi gargadi sosai game da hana mutane fitowa su yi magana a gidan jaridu, inda ya bayyana cewa ba a taba yin lokacin da aka haramtawa ‘yan jarida yin aikin su ba.

Mista Akeredolu ya ke cewa ana samun zaman lafiya ne idan kawai aka ba kowa dama ya fito ya baza hajarsa. Mai girma gwamnan ya kuma ce haka ake tafiya a manyan kasashen Duniya.

A yunkurinsa na kiran a girmama kowane bangaren gwamnati, ya bukaci masu mulki da jam’iyyu su guji yin abin da zai ci karo da ra’ayin gama-garin al’ummar da ake shugabanta.

Mai girma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yi jawabi a taron. Mataimakin gwamnan jihar, Kayode Alabi, shi ne ya wakicli gwamnan a wannan cibiya da ta cika shekara 10.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel