Kauye: Gwamnatin Zamfara ta dauki alkawarin kara wa 'yan bautar kasa alawus

Kauye: Gwamnatin Zamfara ta dauki alkawarin kara wa 'yan bautar kasa alawus

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya ce gwamnatinsa zata fara biyan alawus na musamman ga ‘yan bautar kasar da aka kai kauyukan jihar.

Matawalle ya sanar da hakan ne a ranar Litinin, a sansanin ‘yan bautar kasar jihar da ke karamar hukumar Tsafe, a karshen wayar da kai da aka yi wa ‘yan bautar kasar kashi na uku na 2019.

Ya ce, mulkinsa ya bibiyi duk kokarin ‘yan bautar kasar wajen kokarinsu na ganin sun bada gudummawarsu ga gwamnatin jhar.

“Muna godiya ga NYSC a kokarinsu na ganin suna tayamu habaka jihar nan zuwa mataki mai girma. Mulkina yana matukar godiya kuma zai biya alawus na musamman ga ‘yan bautar kasar da aka tura kauyuka. Wannan hanya ce ta basu kwarin guiwa don su amince yankunan karkarar,”

DUBA WANNAN: Kotu: Maina 'langwai' ya yi, lafiyarsa garau take - Rahoton asibiti

“Zan kuma yi umarni ga kananan hukumomi, masarautun gargajiya da dagatan kauyuka da su karbesu hannu bibbiyu tare da maidasu tamkar ‘yan yankin. Hakan zai ba ‘yan bautar kasar damar sakin jikinsu tare da yin aiyukan da ya dace,” in ji gwamnan.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa gwamnan ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar ne, Alhaji Bala Maru.

Ya shawarci ‘yan bautar kasar da su yi amfani da iliminsu da kuma sana’o’in da suka koya a cikin makonni ukun da suka yi a sansanin, wajen habaka inda aka turasu hidimtawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel