Kama jigo a APC: An barke da zanga-zanga a Zamfara

Kama jigo a APC: An barke da zanga-zanga a Zamfara

- Zanga-zanga ta barke a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara a kan kama wani jigo APC

- Hakan ya faru ne kuwa bayan da jami'an 'yan sanda suka cafke wani hadimin Yari

- Hakan ya biyo bayan mayar wa da Matawalle martani da yayi a kan ikirarin akwai hannun Yari a kashe-kashen jihar

Akwai zanga-zanga da a halin yanzu ta barke a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, a kan kama jigon jam'iyyar APC a jihar, Ibrahim Danmaliki.

An gano cewa, an cafke Danmaliki ne bayan da aka zargesa da yin kalaman da zasu iya tada kayar baya a jihar

Danmaliki ya yi aiki a karkashin tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari, a matsayin mai bada shawara ta musamman a kan al'amura na musamman. Ya yi aiki a matsayin kwamishinan yada labarai karkashin mulkin Mahmuda Aliyu Shinkafi.

DUBA WANNAN: Kotu: Maina 'langwai' ya yi, lafiyarsa garau take - Rahoton asibiti

An ruwaito cewa, 'yan sandan sun tarar da Danmaliki ne har gidansa da ke a Gusau a ranar Litinin. hakan ya biyo bayan martanin da ya mayar wa Gwamna Matawalle a kan zargin Yari da ya yi da daukar nauyin kashe-kashen da ya addabi jihar.

Yace, 'yan bindiga na nan da makamansu har yanzu kuma suna kai hare-harensu duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da ke tsakaninsu da gwamnatin jihar.

Har yanzu dai jami'an 'yan sanda basu yi tsokaci a kan zancen kamen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel