Da duminsa: 'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda guda 2 sun kuma yi garkuwa da mutane 6 a jihar Adamawa

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda guda 2 sun kuma yi garkuwa da mutane 6 a jihar Adamawa

- Wani labari da muke samu yanzu shine yadda wasu 'yan bindiga suka kai harin kwanton bauna akan hanyar Gyella dake jihar Adamawa

- An ruwaito cewa 'yan bindigar sun kashe jami'an 'yan sanda guda biyu sannan kuma sunyi awon gaba da wasu mutane shida da suka tare akan titin

- An bayyana cewa 'yan sandan suna kan hanyarsu ta dawowa daga kai wasu masu laifi babban ofishin 'yan sanda na Mubi ne inda 'yan bindigar suka kai musu hari

Wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne sun kashe jami'an 'yan sanda guda biyu, sannan kuma sunyi garkuwa da mutane shida akan hanyar Gyella dake karamar hukumar Mubi ta Kudu dake jihar Adamawa, wata majiya mai karfi ta bayyanawa jaridar Daily Sun faruwar lamarin a jiya Litinin.

An bayyana cewa 'yan bindigan sun kai harin ne tsakanin karfe 7 zuwa 8 na daren ranar Litinin din, a daidai lokacin da jami'an 'yan sandan suke kan hanyarsu ta dawowa daga babban ofishin 'yan sanda na Mubi a lokacin da suka kai masu laifi.

Jaridar Daily Sun ta bayyana wasu 'yan garin sun kai rahoton wani mutumi bako da ya shigo garin yake sayen kaya da yawa ga ofishin 'yan sanda na Mubi.

Bayan kaiwa 'yan sandan rahoton sai suka bazama neman mutumin, inda kuma suka samu nasarar kamashi da abokananshi suka wuce da su ofishin 'yan sanda na karamar hukumar Mubi ta Arewa.

KU KARANTA: Wani kauye a jihar Kano da bindiga ko wuka ba sa cutar da dan garin

An ruwaito cewa bayan 'yan sandan sun kai wadannan masu laifin ne akan hanyarsu ta komawa wajen aikinsu akan hanyar Gyella 'yan bindigar suka yi musu kwanton bauna, inda suka kashe direban motar 'yan sandan da kuma wani dan sanda daban.

Haka kuma an bayyana cewa 'yan bindigar sun tare motocin wasu mutanen inda suka yi awon gaba da mutane shida.

Idan ba a manta ba makon da ya gabata ne aka sace DPO, Ahidjo Muhammed da kuma dan kasuwa Muhammad Mbilla duka daga karamar hukumar Mubi din, inda har yanzu ake faman neman masu laifin.

Sai dai kuma da aka tuntubi jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar ta Adamawa, Suleiman Nguroje, ya ce: "Ban san da faruwar lamarin ba, amma zanbi kadi na dawo naji gaskiyar lamarin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel