Sowore da Bakare su na neman kotu ta garkame DG Bichi saboda sabawa kotu

Sowore da Bakare su na neman kotu ta garkame DG Bichi saboda sabawa kotu

Shugaban kamfanin gidan jaridar Saharareporters da aka tsare a Najeriya, Omoyele Sowore da kuma Takawaransa, Olawale Bakare, sun shigar da kara kan Darektan DSS, Yusuf Bichi, a kotu.

Omoyele Sowore sun sake maka shugaban hukumar jami’an tsaro na DSS masu fararen kaya a gaban kuliya ne a game da dogon tsare sun da ake cigaba da yi bayan kotu ta nemi a sake su tuni.

Wadanda ke tsaren su na so a daure Yusuf Bichi ne a dalilin kin bin umarnin Alkali mai shari’a Taiwo Taiwo wanda ya fadawa hukumar cewa tsawon lokacin da za a cigaba da tsaresu ya wuce.

Tun cikin Watan Agustan 2019, Jami’an DSS su ka kama Yele Sowore da Wale Bakare bisa wasu zargi da su ka hada har da cin amanan kasa. Wannan ya sa su ka nemi kotu ta shiga lamarinsu.

Dama a kwanakin baya, wadannan Bayin Allah sun yi yunkurin kai karar Yusuf Bichi da Abubakar Malami a kotu, su na neman a biya su Naira miliyan 500 da sunan keta masu alfarma.

KU KARANTA: Wani Fasto ya na tunanin tsayawa Sowore domin a ba shi beli

Jaridar Punch ta bayyana cewa ta ga takardun kotun da wadannan Bayin Allah su ka shirya inda su ke tuhumar DG na hukumar DSS, Yusuf Bichi. Jami’an kotu sun sa hannu a wannan takarda.

Majiyar ta ce an mikawa DSS wadannan kara ta bakin wata daga cikin jami’an ta mai suna Tina James. An sanar da hukumar game da wannan kara ne a Ranar 25 ga Watan Nuwamban 2019.

Lauyoyin masu karar wanda Femi Falana ya ke jagoranta, ya yi wa Bichi barazanar rokon kotu ta daure sa muddin ya cigaba da sabawa umarnin da Alkali ya yi na cewa a saki mutanen biyu.

Wasikar da aka kai wa DG ta na cewa: “Idan ba ka bi umarnin da kotu ta yanke a kara mai lamba FHC/ABJ/CR/235/2019, za a same ka da laifin yi wa kotu bore, kuma za ka cancanta da kurkuku.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel