Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 13, sun kashe direban mota a hanyar Abuja

Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 13, sun kashe direban mota a hanyar Abuja

Wasu gungun miyagun yan bindiga sun dira babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja na jahar Kogi, inda suka tare wata motar bus, suka kashe direban motar, sa’annan suka yi awon gaba da fasinjoji 13 zuwa cikin daji.

Rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:12 na yammacin Litinin, 25 ga watan Nuwamba a daidai kauyen Sabon-Gari inda yan bindigan suka fito daga cikin wani daji sanye da kayan Sojoji.

KU KARANTA: Aiki ga mai kareka: Buhari zai gina asibitoci 8,800 a Najeriya – Ministan lafiya

Wani direba mai suna Ibrahim ya bayyana yadda ya tsallake rijiya da baya, inda yace yana kan hanyarsa ta zuwa kasuwar Kwairta ne bayan ya fito daga garin Abaji, kwatsam sai ya ci karo da yan bindigan sun fito daga daji sanye da kayan Sojoji, nan take suka shiga bude ma motoci wuta.

“A daidai wannan lokaci ne direban wata motar Toyota Highlander Jeep ya yi kokarin tserewa, amma yan bindigan suka bude masa wuta, nan take ya mutu murus. Daga nan sai suka tare wata motar bus da ta fito daga Abuja, inda suka yi awon gaba da fasinjojin motar duka zuwa cikin daji.” Inji shi.

Sai dai da majiyar Legit.ng ta tuntubi kaakakin rundunar Yansandan babban birnin tarayya Abuja, ASP Maryam Yusuf domin jin ta bakinta game da harin, sai tace basu samu wani rahoto game da lamarin ba.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da kama wasu miyagu mutane shida da ake zargi da halaka wata mata, shugabar jam’iyyar PDP, Salome Abu ta hanyar konata da ranta kurmus.

A ranar 18 ga watan Nuwambar 2019 ne wasu miyagu suka afka gidan Salome Abu dake garin Ochadamu a karamar hukumar Ofu na jahar Kogi, inda suka banka ma gidan wuta.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Kogi, DSP William Aya ne ya sanar da kama miyagun su shida a yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Lokoja a ranar Litinin, 25 ga watan Nuwamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel