Oshiomhole ya bukaci Gwmanonin APC su fara aiki da sabon tsarin karin albashi

Oshiomhole ya bukaci Gwmanonin APC su fara aiki da sabon tsarin karin albashi

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Kwamred Adams Oshiomhole, ya roki daukacin gwamnoni da ke kan mulki a karkashin APC da su dabbaka sabon tsarin albashin ma’aikata da aka kawo.

Adams Oshiomhole ya nemi gwamnonin jihohin su fara biyan ma’aikatansu N30, 000 a matsayin mafi karancin albashi. Oshiomhole ya yi wannan kira ne Ranar Litinin dinnan a Garin Jos.

Da yake jawabi a wajen wani zama da manyan jami’an gwamnatin tarayya da gwamnonin APC su ka shirya a Ranar Litinin, 25 ga Watan Nuwamban 2019, Oshiomhole ya yi wannan kira.

“A matsayin mu na masu kawo cigaba, mu zama na farko da za mu fara biyan sabon albashi, kuma ba batun kudin ba kurum, mu dabbaka sababbin kare-karen da aka yi a game da albashin.”

“Yanzu an samu wasu gwamnonin da ba su jiran ta-yi-sanyi, da sun shawo kan wannan batu. Ina rokonku da ku ba wannan muhimmanci, ku fara biyan kudin yayin da wasu ke rikicin biya.”

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta gina kananun asibitoci fiye da 8000 a Najeriya

Shugaban jam’iyyar na APC mai mulki ya ce ya kamata gwamnoninsu su soma biyan ma’aikata wannan sabon tsarin albashi yayin da sauran gwmanonin ke tunanin yadda za su biyan kudin.

Adams Oshiomhole ya kara da cewa: “Idan har kun yi niyya kun ga dama, to za ku iya.” Bayan nan kuma shugaban jam’iyyar ya yi kira ga gwamnoni su ba da goyon-baya kan rufe iyakoki.

Oshiomhole ya na so gwamnanonin APC su marawa matakin da gwamnatin Muhammadu Buhari ya dauka na rufe iyakokin kasa, tare da kira a ba kananan hukumomi gashin-kansu.

Tsohon gwamnan na jihar Edo ya ce za a cigaba da rufe iyakokin har sai lokacin da kasashen da ke makwabtaka da Najeriya su ka bi yarjejeniyar kasuwanci kasa-da-kasa cikin adalci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel