Jiya ba yau ba: Gwamna Masari ya bada labarin yadda Buhari ya shiga aikin Soja

Jiya ba yau ba: Gwamna Masari ya bada labarin yadda Buhari ya shiga aikin Soja

Gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana yadda aka yi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga aikin soja, inda yace Buhari ya samu ra’ayin aikin Soja ne yayin da wasu sojoji suka kai musu ziyara a makarantar sakandari.

Masari ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakoncin babban hafsan soja, kuma darakta a shelkwatar tsaro ta kasa, Kwamanda James Pindar a ofishinsa dake fadar gwamnatin jahar Katsina a ranar Litinin, 25 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Aiki ga mai kareka: Buhari zai gina asibitoci 8,800 a Najeriya – Ministan lafiya

Rahoton jaridar Guardian ta bayyana gwamnan ya yi kira ga Sojoji dasu dinga kai ziyara zuwa makarantun sakandari domin su sanya ma dalibai sha’awar shiga aikin Soja, kamar yadda Buhari ya samu ra’ayin aikin soja a dalilin ziyarar Sojoji makarantarsu.

Haka zalika gwamnan ya kara da cewa hatta janar Hassana Usman Katsina da janar Shehu Musa Yar’adua basu samu sha’awar shiga aikin Soja ba sai bayan wata ziyara da wasu sojoji suka kai zuwa makarantunsu, daga nan ne suka kuduri aniyar zama Sojoji.

Masari yace da irin wadannan ziyara da shelkwatar tsaro ta kaddamar a wancan lokaci ne ta wayar da kawunan dalibai game da muhimmancin aikin soja, kuma ta wannan hanya ne aka samu hazikan yara suka shiga aikin soja da suka bayar da gagarumar gudunmuwa a Najeriya.

“Irin wannan tsari zai kawar da bambamce bambamcen addini dana kabilanci a aikin Soja, sa’annan zai kawar da matsalar bangarenci a gidan Soja.” Inji shi. Sai dai Masari ya yi kira ga hukumar Soji da ta baiwa kowa daman shiga aikin ba tare da dakile wasu ba.

A nasa jawabin, kwamanda Pinder yace sun kai ziyara jahar Katsina ne domin gabatar da jawabai ga daliban makarantun sakandari dana jami’o’i domin wayar musu da kai game da aikin Soja, inda yace tawagarsu ta kunshi hafsoshin Soja uku da kurata 8.

Daga cikin makarantun sakandarin da Sojojin suka halarta akwai makarantar sakandarin yan mata dake Sandamu, kwalejin gwamnatin tarayya Funtua da kuma kwalejin DIkko dake cikin garin Katsina.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel