Kotu: Maina 'langwai' ya yi, lafiyarsa garau take - Rahoton asibiti

Kotu: Maina 'langwai' ya yi, lafiyarsa garau take - Rahoton asibiti

- Kotu ta sanar da cewa Abdulrasheed Maina zai iya jurewa shari'a tare da zaman kotu

- An samo hakan ne daga rahoton bincikar lafiyar tsohon shugaban hukumar fanshon da aka yi

- Kamar yadda rahoton ya nuna, zazzabin cizon sauro ne tare da hauhawar jini ke damunsa

Duk da ganinsa da ake kullum a kotu a kan keken guragu, an musanta rashin lafiyar da ake ikirarin na damun Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa.

Kamar yadda rahoton da gidan gyaran hali suka mika ga babbar kotun tarayya da ke Abuja ya nuna, tsohon shugaban hukumar fanshon ta kasa ya kamu da cutar zazzabin cizon sauro 'yar kadan tare da hawan jini. A saboda hakan, akwai tabbacin zai iya tsayawa har a kare shari'ar.

Rahoton da Remi Ojo ya sa hannu, mataimakin shugaban bangaren lafiya na hukumar, jaridar The Cable ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Kungiyar kamfen din Buhari ta yi martani a a kan sake tsayawarsa takara a karo na uku

Rahoton ya ce, Maina na fama da hauhawar jini amma ya daidaita. "Dukkan sassan jikin Maina masu matukar amfani lafiyarsu kalau, a don haka zai iya jure cigaba da shari'a."

Alkali mai shugabantar shari'ar, Okon Abang, ya bukaci masu gurfanarwa da su mika rahoton ga kungiyar masu kare kansu.

Idan zamu tuna, Legit.ng ta ruwaito cewa an bada belin Maina a kan naira biliyan daya tare da tsayayyu biyu a ranar Litini, 25 ga watan Nuwamba 2019.

Tsohon shugaban hukumar fanshon na fuskantar shari'a ne a kan zarginsa da ake da almundahanar kudi har naira biliyan biyu. Ya kuma isa kotun ne da sanda wacce ke taimaka masa wajen tafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel