Aiki ga mai kareka: Buhari zai gina asibitoci 8,800 a Najeriya – Ministan lafiya

Aiki ga mai kareka: Buhari zai gina asibitoci 8,800 a Najeriya – Ministan lafiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashi takobin gina sabon karamin asibiti a kowanne mazabar siyasa dake cikin kowacce karamar hukuma a dukkanin jahohin Najeriya, kamar yadda ministan kiwon lafiya ya bayyana.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Minista, Dakta Osagie Ehanire ne ya bayyana a yayin taron ranar cutar numoniya ta duniya daya gudana a babban birnin tarayya Abuja, inda yace gwamnatin Buhari za ta samar da karin asibitocin ne domin baiwa yan Najeriya daman samun kulawar kiwon lafiya yadda ya kamata.

KU KARANTA: Na himmatu wajen inganta rayuwar yan Najeriya – cewar shugaba Buhari

Bincikenmu ya nuna idan har hakan ya tabbata, Buhari zai gina sabbin asibitoci akalla guda 8,800 kenan, wanda shi ne karancin adadin mazabun dake cikin kananan hukumomi 774 a jahohi 36, 37 har da babban birnin tarayya Abuja.

Wata kungiyar kasa da kasa ta duniya ce ta zakulo ranar 12 ga wata Nuwamba a matsayin ranar yaki da cutar numoniya, sa’annan tana fafutukar ganin an samar da hanyar da za’a ceci rayuwar miliyoyin kananan yara dake fama da wannan cuta dake kisan mummuke.

A cewar minista: “Wannan cuta tana kashe yaro guda a duk dakikai 20 a duniya, cutar ta fi kashe mutane fiye da cutar sida, zazzabin cizon sauro da bakon dauro, hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO, ta bayyana cewa ana samun mutuwar yara 143,000 a Najeriya a duk shekara daga cutar

“Yawanci wadanda ke mutuwa daga cutar suna yin hakan ne saboda jahilci, ko kuma rashin asibiti a kusa dasu, shi yasa muke muradin samar da asibitoci a kowanne mazaba, ta yadda kowa zai iya samun asibiti daga tafiyar kilomita 5.” Inji shi.

Haka zalika ministan yace zasu kirkiri tsarin daukan jami’an kiwon lafiya daga mazabu wanda aikinsu zai zamo bayar da shawarwari da suka danganci kiwon lafiya ga jama’a, musamman ga mata masu jego, tare da samar da motocin bada agajin gaggawa domin daukan marasa lafiya zuwa asibiti.

Daga karshe ministan ya bada tabbacin Idan har aka cimma wannan tsari, kuma masu ruwa da tsaki suka bayar da goyon baya, zai amfani yan Najeriya sosai da sosai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel