EFCC ta bankado laifin sanatan da ke son a kirkiri dokar amfani da dandalin sada zumunta

EFCC ta bankado laifin sanatan da ke son a kirkiri dokar amfani da dandalin sada zumunta

Wani sanatan Najeriya mai goyon bayan kirkiro dokar kafafen sada zumuntar zamani, ya karba wata kwangilar miliyoyin nairori ba ta hanyar da ta dace ba a lokacin da yake minister, hukumar EFCC ta sanar da hakan a ranar Litinin.

Abba Moro, tsohon ministan cikin gida ne wanda hukumar EFCC ta gurfanar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Hukumar tace, tsohon ministan cikin gidan bai bi hanyar da ta dace ba wajen karbar kwangilar a 2014. Bugu da kari, kwangilar ta yi sanadiyyar rasa rayukan ‘yan Najeriya masu yawa.

Idan zamu tuna, a makon da ya gabata ne Moro ya yi kira ga abokan aikinsa a majalisar dattawa, da su goyi bayan dokar daidaita kafafen sada zumuntar zamani a Najeriya.

A ranar Litinin, shaidar EFCC ya sanar da alkalin yadda aka amincewa Abba Moro kwangilar dibar aikin Nigerian Immigration Service a 2014 ba tare da ya bi hanyoyin da suka dace ba.

DUBA WANNAN: Dokar bayar da kariya ga jakuna ya samu karbuwa a majalisa

Kamar yadda mai magana da yawun hukumar EFCC din ya bayyanawa jaridar Premium Times, ya bayyana yadda Moro karkashin kamfaninsa mai suna Moro and Drexel Tech Nigeria Limited ya karba kwangilar ba tare da bin hanyoyin da suka dace ba. Kwangilar kuma ta yi sanadin rayuka masu yawa a lokacin.

Sanatan ya mika kwangilar ne ga kamfaninsa a yayin da yake ministan cikin gida. Kamar yadda shaidar EFCC din ya sanar, bada kwangilar ta ci karo da dokar bada kwangila ta kasar nan. An yi rijistar neman aikin ne ta yanar gizo. An kuma samu mutane 675,000 da suka yi rijista a kan naira dubu dai-dai. Kudin da yakamata ya shiga asusun gwamnatin tarayya an killacesu ba tare da an saka ba.

EFCC din na tuhumar Moro ne da laifuka 11 da suka hada da damfara tare da almundahanar kudade. An gurafanar dashi ne tare da babban sakataren ma’aikatar, mataimakin daraktan ma’aikatar da kuma kamfanin Drexel Tech Nigeria Limited. An daga sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Janairun 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel