Kungiyar kamfen din Buhari ta yi martani a a kan sake tsayawarsa takara a karo na uku

Kungiyar kamfen din Buhari ta yi martani a a kan sake tsayawarsa takara a karo na uku

Wata kungiyar kamfen din shugaban kasa Buhari, ta ce duk masu tilasta shugaba Buharin don zarcewa mulki a karo na uku, su fidda shi daga hukuncinsu. Don bashi da hannu a lamarin kuma bashi da ra'ayi.

A wata takarda da shugaban kungiyar, Niyi Akinsiju, yasa hannu a ranar Litinin, kungiyar tace duk masu tirsasa shugaban kasar su mutunta shi, kuma su daina wannan kamfen din.

Akinsiju yace, kungiyar ta yarda cewa maganar da shugaban kasar ya fito ya yi, zata sa masu tilastasa su hakura a kashe maganar.

Takardar ta ce, "Muna so mu jaddada cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari gogaggen dan damokaradiyya ne kuma nagartaccen mutum.

"Akwai bukatar mutane su shaida cewa, babban abinda Buhari yasa gaba shine, gyaran bangarorin da suka tabarbare tare da lalacewa a kasar nan, yaki da rashawa tare da tsaftace hanyar da zata billewa 'yan kasa.

"A matsayinsa na mutum mai nagarta, ba zai karya alkawarinsa ba, kuma ba zai gurbata kundin tsarin mulkin kasar nan ba don wata manufarsa, komai kuwa matsin da za a yi.

"Tabbas, zarcewa karo na uku bata daga cikin tsarin shugaban kasar, saboda ya ci karo da rantsuwar da yayi yayin hayewa karagar mulkin kasar nan."

DUBA WANNAN: Yarjejeniyar mayar wa FG $8m: Kotu ta dakatar da EFCC daga gurfanar da Dikko Inde

Idan zamu tuna, Legit.ng ta ruwaito yadda wani mamban jam’iyyar APC a jihar Ebonyi, Charles Oko Enya, ya garzaya babbar kotun tarayya da ke Abakaliki jihar Ebonyi, da bukatar majalisar dattawa da ministan shari’ar Najeriya, Jastis Malami, su cire duk wani shinge a kundin tsarin mulkin Najeriya da ya haramtawa shugaban kasa da gwamnoni neman zarcewa a karo na uku.

A karar mai lamba FHC/AI/CS/90/19, wacce aka shigar a ranar Laraba da ta gabata kuma aka bayyana ga manema labarai, lauyan mai karar, Barista Iheanocho Agboti, ya bukaci sauyi a sashi na 137, sakin layi na 1 da kuma sashi na 182, sakin layi na daya na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel