Karya ta kare: Miyagun da suka halaka shugabar matan jam’iyyar PDP sun shiga hannu

Karya ta kare: Miyagun da suka halaka shugabar matan jam’iyyar PDP sun shiga hannu

Rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da kama wasu miyagu mutane shida da ake zargi da halaka wata mata, shugabar jam’iyyar PDP, Salome Abu ta hanyar konata da ranta kurmus.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito a ranar 18 ga watan Nuwambar 2019 ne wasu miyagu suka afka gidan Salome Abu dake garin Ochadamu a karamar hukumar Ofu na jahar Kogi, inda suka banka ma gidan wuta.

KU KARANTA: Gwamnatin Kaduna za ta rugurguza gadar sama dake Kawo don gina sabuwa

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Kogi, DSP William Aya ne ya sanar da kama miyagun su shida a yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Lokoja a ranar Litinin, 25 ga watan Nuwamba.

Kaakakin ya bayyana cewa jami’an Yansandan sun kama miyagun ne a ranar Juma’a, 22 ga watan Nuwamba, inda yace sun fara gudanar da cikakken bincike a kan mutanen domin su gano iya rawar da suka taka wajen kisan matar.

A ranar Lahadi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Yansanda su tabbata sun kama miyagun da suka kashe wannan matar domin su tabbatar da an hukuntasu kamar yadda doka ta tanada.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Osun ta sanar da kama wata mata mai suna Rukayat Abulraheem mai shekaru 33 a garin Osogbo, babban birnin jahar Osun biyo baya zarginta da ake yi da halaka dan cikinta.

Har yanzu babu tabbataccen hujja da uwar ta bayar na aikata ma dan da ta haifa wannan aika aika, amma Yansanda sun bayyana matar ta kashe Abdulganiyu ne a ranar 17 ga watan Nuwamba ta hanyar hankada shi cikin rijiya.

Sai dai bayan Yansanda sun kamata, sun gudanar da bincike a kanta, sa’annan suka gurfanar da ita gaban kotu a ranar Juma’ar da ta gabata, amma a yayin zaman kotun, sai lauyanta, Galadima Adeoye ya bukaci Yansanda su je su sake gudanar da bincike yadda ya kamata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel