Yadda gwamna ya gayyato bokayen kasar Indiya don su bashi nasara a zabe – mataimakin gwamna

Yadda gwamna ya gayyato bokayen kasar Indiya don su bashi nasara a zabe – mataimakin gwamna

Sabon zababben mataimakin gwamnan jahar Bayelsa, Sanata Biobarakuma Degi ya bayyana cewa dan takarar gwamnan Bayelsa na jam’iyyar PDP Douye Diri ya fadi zabe ne saboda maigidansa gwamnan jahar mai barin gado, Seriake Dickson ya dauko hayan bokaye daga Indiya.

Sabon zababben mataimakin gwamnan dan jam’iyyar APC ya bayyana haka ne a garin Calabar yayin da yake ganawa da abokan arziki, inda yace ya fi a kirashi da suna ‘Ambo boy’ saboda dadewar da yayi a titin Ambo bayan ya kammala wa’adinsa a matsayin shugaban karamar hukumar Nembe.

KU KARANTA: Gwamnatin Kaduna za ta rugurguza gadar sama dake Kawo don gina sabuwa

Daily Trust ta ruwaito Degi ya cigaba da cewa Gwamna Dickson ya shigo da dimbin bokaye da matsafa daga kasar indiya, inda ya tarasu a fadar gwamnatin jahar Bayelsa yana biyansu makudan kudade.

Degi yace an shigo dasu ne ba don komai ba sai domin su yi ma jama’an jahar Bayelsa asiri ta yadda zasu zabi dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP tare da kare masu aiki a ofishin gwamnan jahar.

“Duk da irin makudan kudaden da yan siyasan jam’iyyar adawa ta PDP suka kashe, sun shigo da muggan matsafa daga Indiya, tare da wasu bokayen gida duk domin su samu nasara, amma basu yi nasara ba saboda jama’a sun yi tirjiya, sun zabi wanda suke so.

“Bamu da kwatankwacin kudaden da suka kashe, mun dogara ga Allah ne kawai, Allah kuma ya fi karfin duk wani boka ko matsafi da suka shigo dasu daga kasar Indiya, kuma Allah bai bamu kunya ba.” Inji shi.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Ogun ta sanar da kama wata mat yar shekara 42 mai suna Temitope Akinola biyo bayan zarginta da ake yi da kwankwada ma jaririyar diyarta fiya fiya bayan kwanaki biyu kacal da haihuwarta.

Kaakakin Yansandan Ogun, Oyeyemi yace mahaifiyar jaririyar ta bar jaririyar ne a hannun kulawar babarta, inda ta shiga bandaki domin ta yi wanka, amma koda ta dawo, sai dai kawai ta tarar da gawar diyar kwance ba rai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel