Yanzu-yanzu: Kotu ta baiwa Maina belin bilyan daya

Yanzu-yanzu: Kotu ta baiwa Maina belin bilyan daya

Babban kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta baiwa Mista AbdulRashid Maina, belin naira bilyan daya tare da mutane biyu da zasu tsaya masa.

Alkalin kotun, Jastis Abang, ta bayyana cewa wajibi ne mutanen zasu tsaya masa su kasance Sanatoci.

Hakazalika, ya ce wajibi da sanatocin biyu su kasance masu gidaje a unguwar Maitama ko Asokoro a cikin birnin tarayya Abuja.

Unguwannin Maitama da Asokoro ne suka fi yawan masu kudi da tsadan gidaje a Abuja.

Bugu da kari, Alkalin ya bayyana cewa wajibi da masu tsaya masa su mika takardan shaidan biyan kudin haraji na tsawon shekaru uku da suka gabata kuma su hallara a kotu a duk ranar da kotu ta bukaceshi.

Abin bai kare ba, Alkalin ya ce wajibi ne masu tsaya masa su rantse cewa zasu iya biyan kudin belin.

KU KARANTA: Wasu marasa kishin kasa na yi mini zagon kasa - Sheikh Isa Pantami

A karshen makon da ya gabata, Iyalin Abdulrasheed Maina sun yi kira ga shugaban babban kotun tarayya,Jastis John Tsoho a kan ya canza alkalin da ke shari'a tsakanin gwamnatin tarayya da Faisal Abdulrasheed Maina saboda basu yarda da Jastis Okon Abong na babbar kotun tarayya ta 6 da ke Abuja ba.

Hukumar EFCC da zargin Maina da almundahanar kudin fanshon al'umma na biliyoyin nairori. An kwashe shekaru bakwai ana nemansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel