Wasu marasa kishin kasa na yi mini zagon kasa - Sheikh Isa Pantami

Wasu marasa kishin kasa na yi mini zagon kasa - Sheikh Isa Pantami

Ministan sadarwa, Sheikh Dakta Isa Ali Pantami, ya yi gargadi ga wasu marasa kishin kasa dake kokarin yiwa ma'aikatarsa zagon kasa kan ayyukan walwalan jama'an da suke yiwa yan Najeriya.

Malam Pantami, ya yi wannan gargadi ne ta bakin mai magana da yawunsa, Uwa Suleiman, a jawabin da ta saki ranar Litinin a Abuja.

A jawabin yace binciken da aka kaddamar kan wasu masu almundahana ya sa suna kokarin yada labaran karya kan ma'aikatar.

Ministan ya ce wadannan mutane sun fara kokarin bata masa suna saboda basu jin dadin irin canjin da ya kawo ma'aikatar domin jin dadin al'umma.

"Abinda mutanen nan ke shirin yi shine baiwa yan jarida kudi domin yada labaran karya saboda mu barsu su cigaba da cutan yan Najeriya."

"Sabbin dokokin da muka kawo ya fara baiwa wasu masu ruwa tsaki haushi kuma suna kokarin yiwa hakan zagon kasa."

DUBA NAN: Kotu ta baiwa Maina belin bilyan daya

Ya yi kira ga yan jarida su yi watsi da duk wani abin da zai gurbata musu aikinsu kuma su rike mutuncinsu.

Malam Pantami ya tabbatarwa yan Najeriya cewa ba zai gajiya wajen yaki da rashawa da rashin adalcin da masu hannu da shuni ke yiwa yan Najeriya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel