Yanzu-yanzu: Tun bayan zabe da ya bar Najeriya, Atiku ya dawo gida

Yanzu-yanzu: Tun bayan zabe da ya bar Najeriya, Atiku ya dawo gida

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP a zaben shugaban kasan 2019, Atiku Abubakar, ya dawo Najeriya a ranar Litinin, 25 ga Nuwamba, 2019. Thisday ta ruwaito.

Hadimin Atiku, Paul Ibe, ya bayyana hakan ga manema labarai.

A cewar Mista Ibe, tsohon mataimakin shugaban kasan ya dawo da safen nan bayan kwashe watanni a kasar waje.

Yace: "Gobe Talata, zai je Yola, jihar Adamawa domin gaisuwar ta'aziyya ga iyalan hadiminsa da ya mutu. Duk da cewa an riga an birneshi."

Hakazalika, yau ya cika shekaru 73 a duniya.

DUBA NAN: Hotunan bikin daurin auren matashin da ya auri yan mata uku rana daya

A cikin kwanakin da ya tafi Dubai, shugaba Buhari ya samu nasara kan Atiku da jam'iyyarsa ta PDP a kotun daukaka kara da kotun koli inda yake kalubalantar da nasarar Buhari a zaben Febrairun 2019.

Atiku da lauyoyinsa sun zargi Buhari da rashin kammala karatun sakandare kuma saboda haka, ba cancanci takaran kujeran shugaban kasa ba.

Kotun kolin Najeriya ta bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi daidai wajen rashin baiwa hukumar gudanar da zaben ta kasa wato INEC kwalayen karatunsa.

Kotun ta bayyana hakan ne yayinda take zayyana dalilan da yasa tayi watsi da karar jam'iyyar PDP da dan takararta, Atiku Abubakar, a ranar Juma'a, 15 ga Nuwamba, 2019.

Manyan Alkalan sun yi ittifakin cewa ko babu kwalin karatu shugaba Buhari ya cancanci takarar kujeran shugaban kasa.

Kotun ta yanke cewa sabanin abinda PDP take ikirari, babu dokar da ta bukaci dan takara ya gabatar da kwalayen karatunsa ga hukumar INEC kafin ta amince yayi takara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel