Ainihin abin da ya sa APC ta karbe Jihar Bayelsa – Ambasada Igali

Ainihin abin da ya sa APC ta karbe Jihar Bayelsa – Ambasada Igali

Jigon PDP, Godknows Igali ya yi hira da ‘yan jarida a game da zaben Bayelsa, ya ce tun farko alamu sun nuna za ta bare da su a zaben 2019, don haka ne ma ya rika jan-kunnen ‘yan jam’iyya.

Tsohon Sakataren na din-din-din a gwamnatin tarayya ya ce PDP ta zama ta sakata ta na ganin cewa babu abin da zai sa ta fadi zabe, amma a karshe ta sha kayi a jihar da ba ta taba rasawa ba.

Igali ya ce kowane bangaren jihar Bayelsa ya samu mulki daga lokacin Diepreye Alamieyeseigha, Goodluck Jonathan, Timipre Sylva zuwa Seriake Dickson wanda ya fara yin shekaru 8 a gwamna.

Tsohon jami’in ya nuna yadda na-kusa da gwamna mai-ci su ka nemi su yi watsi da tsarin kama-kama inda irin su Sylvester Ikoli, David Alagwa da Fred Agbedi su ka yanki fam din takara a PDP.

Don haka ne aka bada dama wannan karo mulki ya koma ga mutanen tsakiyar Bayelsa. Igali ya ce an fito da mutumin Kolokuma a zaben Sanata da tunanin za a ba mutanen Ijaw gwamna.

Sai dai kuma ba hakan aka yi ba, duk da cewa Sanatan tsakiya ya fito daga karamin Garin Kolokuma, sai aka hana ‘yan siyasar Ijaw takarar gwamna a karkashin PDP inji Jigon na PDP.

KU KARANTA: Yaudara a jinin PDP ya ke – Sule ya yi magana a kan zaben Bayelsa

“Kwatsam ana haka sai mu ka ga Douye Diri wanda mu ka zaba a matsayin Sanata ya saye fam. Sai kuma aka kara kudin fam daga miliyan 10 zuwa miluyan 21. Haka ‘yan takara 21 su ka biya.”

Ambasadan ya ce: "Daga nan mu ka fara kokawa a yankinmu, da jiha da kuma gaban uwar-jam’iyya, amma aka yi gum ba ayi komai ba. Lokacin zabe sai mu ka ji gwamna na da ‘dan takara”

A cewar Igali, Diri ya na damar sayen fam, kuma gwamna ya isa ya tsaida ‘dan takara. Sai dai ya ce Uba bai dace ya nuna fifiko a tsakanin ‘Ya ‘yansa a cikin gida karara ba, idan za a zauna lafiya.

“Bayan nan sai gwamna ya ce mu yi azumin kwanaki uku a game da zaben fitar da gwanin. Da gama azumi sai mu ka ji gwamna ya tsaida wasu gungun ‘yan takararsa na mutum uku rak.

Wannan son-kai na gwamna mai barin-gado ya na cikin abin da ya hallaka PDP a jihar a cewar Igali. A cikin ‘yan takara 21, gwamnan ya nuna fifiko wanda a karshe wasu su ka juya masa baya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel