Yarjejeniyar mayar wa FG $8m: Kotu ta dakatar da EFCC daga gurfanar da Dikko Inde

Yarjejeniyar mayar wa FG $8m: Kotu ta dakatar da EFCC daga gurfanar da Dikko Inde

- Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta hana hukumar yaki da rashawa ta EFCC gurfanar da tsohon shugaban hukumar kwastam, Abdullahi Inde Dikko

- Kotun ta yanke hukuncin ne bayan yarjejeniyar da ke tsakanin gwamnatin tarayya da Dikko a kan mayar da dala miliyan takwas

- Alkalin kotun ya ce, Dikko ya cigaba da cika alkawarin da ke tsakaninsu ta hanyar mayar da wasu makuden kudade ga asusun EFCC da ke babban bankin Najeriya

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Litinin, 25 ga watan Nuwamba, ta dakatar da hukumar yaki da rashawa ta EFCC daga gurfanar da Abdullahi Inde Dikko, tsohon shugaban hukumar kwastam.

Dikko na fuskantar zargi a kan wasu makuden kudade ne da ya waskar tun yana shugabantar hukumar.

DUBA WANNAN: Sake zabe: PDP da Dino Melaye sun yi watsi da sabuwar ranar zaben kujerar sanatan Kogi ta Yamma

An gano cewa, kotun ta haramtawa EFCC gurfanar da Dikko saboda yarjejeniyar da suka yi da ministan shari'a da shugaban hukumar jami'an tsaro ta farin kaya, a kan cewa zai mayar wa gwamnatin tarayya dala miliyan takwas.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, tsohon shugaban hukumar kwastam din ya cika alkawarinsa don ya mayar wa da gwamnantin tarayya 1,576,000,000 ta asusun samo kudade na EFCC da ke babban bankin Najeriya.

A don haka ne mai shari'ar ya jaddada cewa, hukumar yaki da rashawa ta EFCC ko ire-irenta a fadin kasar nan ba zasu gurfanar da Abdullahi Dikko Inde ba a kan makamancin laifin.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito yadda aka shigar da karar Abdullahi Dikko tare da wasu mutane biyu a gaban wata babban kotun tarayya da ke Abuja a kan satar naira biliyan daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel