Matawalle ya janye barazanarsa ga Yari, ya gindaya sharadi

Matawalle ya janye barazanarsa ga Yari, ya gindaya sharadi

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ce Abdulaziz Yari zai iya kawo ziyara jihar Zamfara, matukar zai zama dan kasa mai bin doka.

Gwamnan ya sanar da hakan ne ta bakin darakta janar din yada labaransa, Alhaji Yusuf Idris, ya ce Yari zai iya ziyartar jihar, matukar ba zai lalata kokarin gwamnatin jihar wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar ba.

A baya dai Matawalle ya ja kunnen tsohon gwamnan a kan ya daina ziyartar jihar ko kuma ya fuskanci fushin hukuma. Kamar yadda yace, ana samun matsalar tsaro a duk lokacin da tsohon gwamnan ya kawo ziyara jihar, zargin da tsohon gwamnan ya musanta ta bakin hadiminsa.

Idris ya jaddada cewa, Matawalle bai umarci tsohon gwamnan da ya daina zuwa jihar kwata-kwata ba.

DUBA WANNAN: Sake zabe: PDP da Dino Melaye sun yi watsi da sabuwar ranar zaben kujerar sanatan Kogi ta Yamma

Ya ce, ”Abinda ya ce shine, kada ya zamo kalubale ga kokarin gwamnatin jihar na tabbatar da tsaro. Munsan tsohon gwamnan na da damar zuwa inda yake so ballantana a jihar Zamfara. Matawalle bai ce kada ya zo Zamfara ba, amma sharadi daya ne, ya mutunta dokar jihar. Dokar jihar ta haramta taron siyasa a yanzu. Idan kuwa ya gwada karya doka, zai fuskanci hukuncin da ya dace.”

Ya tabbatar da cewa, jihar ta fara morar romon zaman lafiya tun bayan da Matawalle ya hau karagar mulkin jihar

Ina kalubalantar ‘yan adawa da su nuna wani sashi na jihar nan da ke fuskantar kalubalen tsaro a da, kuma yanzu yana cikin halin,” Idirs ya ce.

Ya tabbatar da cewa, duk wadannan abubuwan sun zama tarihi, yayin da ‘yan kasuwa da sauran ‘yan jihar ke cigaba da halastattun kasuwancinsu. Tituna da kasuwannin da aka rufe tuntuni yanzu duk an budesu sun cigaba da harkokinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel