Farfesa Is-haq Oloyede zai samu lambar yabon NPOM daga Shugaban kasa

Farfesa Is-haq Oloyede zai samu lambar yabon NPOM daga Shugaban kasa

The Nation ta ce shugaban hukumar nan ta JAMB mai shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare, Farfesa Is-haq Oloyede zai karbi lambar yabo daga hannun shugaban kasa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi Farfesa Is-haq Oloyede a matsayin wanda zai samu lambar yabo na musamman na NPOM, tare da wasu masu kishin-kasa saboda irin kokarin da su ka yi.

Jaridar ta fito da wannan rahoto ne bayan mujallar mako-mako ta hukumar JAMB ta bayyana wannan labari a Ranar Lahadi, 24 ga Watan Nuwamban 2019 ta bakin Mai magana da yawunta.

Fabian Benjamin wanda ya ke magana a madadin JAMB, ya shaida cewa an zabi Is-haq Oloyede matsayin wanda zai lashe wannan kyauta ne a wata wasika da Ministan kwadago ya aiko masa.

Dr. Chris Ngige ya shaidawa shugaban hukumar jarrabawar cewa Mai girma Muhammadu Buhari zai karrama shi da babbar lambar yabo na kasa NPOM tare da wasu Bayin Allah da su ka yi zarra.

KU KARANTA: Jami'ar Katsina ta yi magana a kan Ma’aikacinta da aka sace

Wasikar Ministar kwadagon Kasar ta ce: “Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya amince da ba ka kyautar NPOM a dalilin kwazo da himma da kokarinka da aka gani wajen aiki”

Wasu daga cikin kokarin Farfesan da aka gani sun hada da aiki ke-ke-ke-ke a hukumar JAMB, da kawo gaskiya da amfani da na’urori da fasahar zamani wajen tafiyar da harkar jarrabaawa.

Mujallar hukumar ta ce wannan gwamnati mai yaki da rashin gaskiya ta ga irin aikin da shugabanta ya ke yi na wallafa duk kudin da ake kashewa tare da kokarin rike amanar jama'a.

Yanzu haka, Oloyede shi ne shugaban kungiyar NIREC ta addinan Najeriya. Haka zalika shi ne shugaban kungiyar Jami’o’in Afrika a matsayinsa na tsohon shugaban shugaban UNILORIN.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Online view pixel