Alfahari: Ko da bana majalisa, kaakakin majalisa ya bani motoci guda 3 – Alhassan Doguwa

Alfahari: Ko da bana majalisa, kaakakin majalisa ya bani motoci guda 3 – Alhassan Doguwa

Tsohon dan majalisar jahar Kano dake wakiltar mazabar Tudunwada/Doguwa a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa kaakakin majalisar wakilai, Femi Ggajabiamila ya bashi kyautan motoci guda uku duk da cewa kotu ta tsige shi daga kan kujerar.

Doguwa ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo da jaridar Daily Nigerian ta gano, inda yake ganawa da al’ummar mazabarsa, yana cika baki cewa shugabancin majalisa da shugabancin jam’iyya sun amince ba za su maye gurbinsa ba har sai bayan gudanar da zabe.

KU KARANTA: Rashin Imani: Miyagu sun shafe wasu iyalai gaba daya a jahar Benuwe

Idan za’a tuna, Doguwa shi ne tsohon shugaban masu rinjaye na majalisa, kuma a ranar 4 ga watan Nuwamba ne wata kotun daukaka kara dake zamanta a Kaduna ta soke zabensa, inda ta umarci INEC ta shirya wani zaben.

Sai dai Doguwa yace tun da har kaakakin majalisa ya bashi motoci guda uku domin gudanar da aikace aikacensa, hakan na nufin har yanzu majalisa na kallonsa a matsayin shugaban masu rinjaye duk da hukuncin kotu, don haka ta bashi motoci kamar yadda ake baiwa kowa.

“Abokan hamayya ne sun yi mamaki, kwanaki uku da suka gabata, daidai kwanaki 16 kenan da bari na majalisa, na dawo daga wata tafiya sai na tarar da sabbin motoci guda uku a gidana daga majalisa ta aiko ma shugaban masu rinjaye, idan ka duba gidana dake Apo, za ka gansu.

“Wannan matakin bani motoci na nufin shugabancin majalisa da shugabancin jam’iyya sun amince ba za su maye gurbina da wani ba har sai bayan gudanar da zabe.” Inji shi.

Daga karshe Doguwa ya karkare jawabinsa da cewa “Ba’a taba samun irin haka a siyasar Najeriya, ko a karamar hukuma, da zarar an soke zaben kansila, cikin sa’o’i 28 ake maye gurbinsa da wani.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel