Kowa ya bar gida, gida ya bar shi: Atiku zai dawo Najeriya ranar da ya cika shekaru 73

Kowa ya bar gida, gida ya bar shi: Atiku zai dawo Najeriya ranar da ya cika shekaru 73

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya kammala balaguron daya tafi zuwa kasar Dubai, inda a yau a ke sa ran dawowarsa gida Najeriya.

Jaridar Blueprint ta ruwaito Atiku zai dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 25 ga watan Nuwamba, bayan kwashe kusan watanni 5 a kasar Dubai yana hutawa tare da gudanar da sha’aninsa daban daban.

KU KARANTA: Rashin Imani: Miyagu sun shafe wasu iyalai gaba daya a jahar Benuwe

Bugu da kari, ranar 25 ga watan Nuwamba ne ya yi daidai da ranar haihuwar tsohon mataimakin shugaban kasa, sai dai majiyoyi tabbatattu sun tabbatar da cewa ba za a yi wani shagalin bikin murnar cikarsa shekaru 73 ba.

Ko a ranar murnar zagayowar ranar haihuwarsa na shekarar da ta gabata, Atiku ya dakatar da danginsa, yan uwa da abokansa na arziki daga shirya masa wani shagalin biki, inda ya nemi su sadaukar da duk kudin da za su kashe wajen shagalin ga gidajen marayu.

A wani labarin kuma, Atiku Abubakar ya yi babban rashin babban hadiminsa, kuma na hannun dama, Alhaji Jidda Pariya, wanda Allah Ya dauki ransa a makon da ta gabata a kasar Dubai bayan wata gajeruwar rashin lafiya.

Yan Najeriya da dama sun yi ma tsohon mataimakin shugaban kasa ta’aziyyar mutuwar Pariya tare da taya shi jimami da alhinin rashin da ya yi, daga ciki har da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya yi addu’ar Allah Ya gafarta ma Jiddo, Ya kuma baiwa su Atiku hakurin rashinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel