Sake zabe: PDP da Dino Melaye sun yi watsi da sabuwar ranar zaben kujerar sanatan Kogi ta Yamma

Sake zabe: PDP da Dino Melaye sun yi watsi da sabuwar ranar zaben kujerar sanatan Kogi ta Yamma

- Akwai alamun jam'iyyar PDP ba zasu fito zaben ranar 30 ga watan Nuwamba ba na kujerar sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma

- Mai magana da yawun PDP din, yace jam'iyyar a halin yanzu ba ta gamsu da ikirarin INEC na yi zaben gaskiya ba

- Ologbondiyan, ya ce sun yi watsi da sabuwar ranar sauya zaben, saboda ba zata fito da bukatar masu kada kuri'a ba

A yayin da hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta saka ranar Asabar, 30 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a kara yin zaben kujerar sanata mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, akwai alamun Dino Melaye da PDP ba zasu fito zabe ba.

Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune fa fitar, sakataren yada labarai na PDP, Kola Ologbondiyan, yace jam'iyyar a halin yanzu bata gamsu da cewa shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, zai iya yin zabe na gaskiya ba.

An ruwaito cewa, Ologbondiyan ya kara da cewa, jam'iyyar PDP ta yi watsi da sabuwar ranar zaben. Ya bayyana cewa, akwai yuwuwar ba zasu fito zaben ba.

"Mun yi watsi da sabuwar ranar sake zaben kujerar sanatan Kogi ta yamma, saboda an riga an lalata sakamakon zaben tun farko," in ji wani sashi na takardar.

DUBA WANNAN: Rusau: KASUPDA ta rushe gidaje 300 a Kaduna

Tuni dai jam'iyyar APC ta zargi cewa, an yi kuskure tun a asalin zaben, sakamakon zaben da aka sake yi ne ya bayyana gaskiyar ra'ayin masu kada kuri'a.

Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa, har yanzu 'yan jam'iyyar na fama da alhini tare da makokin mambobinsu da aka hallaka a ranar 16 ga watan Nuwamba yayin sake zaben.

Idan zamu tuna, Legit.ng ta ruwaito cewa a ranar Laraba, Dino Melaye ya mika koke ga hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC a Abuja, da bukatar a soke zaben sanatan yankin jihar Kogi ta Yamma.

Dan majalisar ya wallafa a shafinsa na tuwita yadda ya mika bidiyoyi 21 tare da kokensa. Bidiyoyin na bayyana yadda aka tafka magudin zabe a yankin.

Sanatan ya ce, ya samu tarba ne daga sakatariyar INEC, Rose Orianran-Anthony da kuma kwamishinan hukumar na kasa Festus Okoye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel