Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya yi wa Iyalan Kyaftin Richard Edorhe ta’aziyya

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya yi wa Iyalan Kyaftin Richard Edorhe ta’aziyya

A kwanakin baya ne Kyaftin Tunde Richard Edorhe ya bar Duniya ya na da shekaru 50. Richard Edorhe ya yi kaurin suna ne wajen tuka jiragen da ke cikin fadar shugaban kasa a Najeriya.

Marigayin ya rasu ne a Ranar 22 ga Watan Oktoban 2019 a Garin Kennesaw a kasar Amurka. An yi jana’izar sa ne a Ranar 16 ga Watan Nuwamba a asibitin Sr. Joseph da kecikin birnin Marietta.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci Iyalin mamacin a matsayinsa na wanda ya yi shekaru fiye da 19 ya na bautawa fadar shugaban kasa a matsayin Direban jirgi.

Marigayi Kyaftin Richard Edorge ya na cikin manyan masu tuka jiragen da ke fadar shugaban kasa. A lokacin ya na raye, Edorge ya tuka shugabannin kasashe guda hudu da aka yi a Najeriya.

Haka zalika Marigayi Richard Edorhe ya tuka mataimakan shugaban kasa a Najeriya a lokacin da ya ke bakin aiki. Daga cikin manyan Fasinjojinsa akwai shi kansa Mai girma Yemi Osinbajo.

KU KARANTA: An gano hanyar da ake fasa kwaurin shinkafa a Najeriya

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya yi wa Iyalan Kyaftin Richard Edorhe ta’aziyya

Osinbajo ya wakilci Gwamnatin Shugaba Buhari wajen ta'aziyyar Edorhe
Source: UGC

Tunde Richard Edorhe ya soma tukin jirgi a fadar shugaban kasar ne a Junairun 2000. Hakan na nufin ya shafe shekara 19 da watanni goma sha daya a matsayin Direban jirgin sama a fadar.

Kamar yadda wasu hotuna daga Mai daukar mataimakin shugaban kasar hoto watau Tolani Alli su ka nuna, Osinbajo ya ziyarci Iyalin Marigayin ya jajanata masu a madadin gwamnatin kasar.

An haifi Marigayi ne a Junairun 1969 a Garin Kaduna. Ya yi karatunsa ne a jihar Kaduna da Kwara, kafin ya shiga harkar Lauya. Daga baya ya ajiye wannan ya shiga bangaren jirgin sama.

Edorhe ya fara karatun koyon tukin jirgi tun yana shekara 18 a makarantar koyon tukin jirgin nan da ke San Fransico a California. Ya fara aiki da jirgin Kabo a 1990 kafin ya koma Matukin fada.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel