Mamba a APC ya garzaya kotu neman ta tilasta wa Buhari takara a 2023

Mamba a APC ya garzaya kotu neman ta tilasta wa Buhari takara a 2023

Wani mamban jam’iyyar APC a jihar Ebonyi, Charles Oko Enya, ya garzaya babbar kotun tarayya da ke Abakaliki jihar Ebonyi, da bukatar majalisar dattawa da ministan shari’ar Najeriya, Jastis Malami, su cire duk wani shinge a kundin tsarin mulkin Najeriya da ya haramtawa shugaban kasa da gwamnoni neman zarcewa a karo na uku.

A karar mai lamba FHC/AI/CS/90/19, wacce aka shigar a ranar Laraba da ta gabata kuma aka bayyana ga manema labarai, lauyan mai karar, Barista Iheanocho Agboti, ya bukaci sauyi a sashi na 137, sakin layi na 1 da kuma sashi na 182, sakin layi na daya na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Ya jaddada cewa, sassan na kundin tsarin mulkin, sun dakile hakkokin irinsu shugaban kasa Muhammadu Buhari, tare da duk gwamnonin jihohi amma banda ‘yan majalisu.

DUBA WANNAN: Rusau: KASUPDA ta rushe gidaje 300 a Kaduna

Masu kare kansu a karar sune: magatakardan majalisar dattawa, Mohammed Sani Omolori da ministan shari’ar Najeriya, Abubakar Malami.

Enya, wanda yake jiran lokacin da kotun zata fara sauraron shari’ar, yace yana bukatar kotun da ta umarci masu kare kansu da su goge sassan kundin tsarin mulkin kasar nan da ya hana Buhari da gwamnoni zarcewa karo na uku.

Ya ce, “Ina bukatar kotu da ta shafe tanadin sashi na 137, sakin layi na daya da kuma sashi na 182 sakin layi na daya na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel